Buhari ya girgiza: Mutuwar Deby ta haifar da ‘Babban Gurbi’ a yaki da Boko Haram

Buhari ya girgiza: Mutuwar Deby ta haifar da ‘Babban Gurbi’ a yaki da Boko Haram

- Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harbe shugaban kasar Chadi da aka yi

- Ya kuma mika ta'aziyya ga iyalai da ilahirin al'ummar kasar Chadi bisa wannan babban rashi

- Karshe ya bayyana cewa, rashin shugaban zai haifar da babban gurbi a kokarin yaki da Boko Haram

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya ce rasuwar shugaban kasar Chadi Idriss Deby "tabbas zai haifar da babban gurbi a kokarin da ake yi na hada karfi da karfe wajen tunkarar 'yan ta'addan Boko Haram da kuma Daular Musulunci ta Afirka ta Yamma."

Shugaban ya yi wannan bayanin ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin sa Garba Shehu, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Deby ya mutu ne sakamakon raunin da ya samu yayin fada da ‘yan tawaye a arewacin kasar, a cewar sojojin Chadi a safiyar ranar Talata.

KU KARANTA: 'Yan sandan Najeriya 144 sun isa Somaliya domin tabbatar da tsaro

Mutuwar Deby ta haifar da ‘Babban Gurbi’ a yaki da Boko Haram, in ji Buhari
Mutuwar Deby ta haifar da ‘Babban Gurbi’ a yaki da Boko Haram, in ji Buhari Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Wannan sanarwar mai ban tsoro ta zo ne kwana daya kacal bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da ya ba shi damar wa’adin mulki na shida.

Da yake maida martani kan lamarin ranar Talata, Shugaba Buhari ya ce "ya yi matukar kaduwa da dimautuwa game da mutuwar kwatsam ta Idriss Deby a fagen daga don kare 'yancin kasarsa."

A cewar shugaban, "Marigayi Deby ya taka rawar gani a hadin gwiwar yankin da muke da shi a yakin soja kan 'yan ta'addan Boko Haram."

Ya kara da cewa "mutuwar Deby tabbas za ta haifar da babban gurbi a kokarin hada karfi da karfe don tunkarar 'yan ta'addan Boko Haram da kuma Daular Musulunci ta Afirka ta Yamma."

Yayin da yake jajantawa mutanen Chadi da sabon shugabansu, Shugaba Buhari ya yi kira da a kara hadin gwiwa domin fatattakar ‘yan ta’addan.

KU KARANTA: Wata kungiyar Kiristoci ta yi Allah wadai da kagen da aka yiwa Dr Pantami A wani labarin, A makon nan ne ake jimamin mutuwar Idriss Déby Itno. Kafin rasuwarsa, ya kasance shugaban Chad, wanda ya shafe sama da shekara 30 a mulki.

Legit.ng Hausa ta tsakuro wasu bayanai a kan tarihin rayuwar Idriss Déby Itno daga shafin Britanica.

Asali: Legit.ng

Online view pixel