Cikin kwanaki 4 ku mika wuya ko ku fuskanci fushin gwamnati, Matawalle ga 'yan bindiga

Cikin kwanaki 4 ku mika wuya ko ku fuskanci fushin gwamnati, Matawalle ga 'yan bindiga

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya zargi wasu 'yan bindiga da yaudara gwamnati

- Gwamnan ya ce ya samar da wata sabuwar dabara ta tsaro domin kiyaye mazauna yankin

- 'Yan bindiga sun mamaye wasu garuruwa a jihar ta Zamfara tare da hallaka mutane da dama

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya gargadi 'yan bindiga a jihar da su tuba ko kuma su fuskanci mummunan mataki daga gwamnati.

Gwamnan a ranar Asabar, 24 ga Afrilu, ya bayyana cewa ya tsara sabuwar taswira a yadda yake tunkarar matsalar tsaro da ke addabar jihar, a cewar wata sanarwa daga mai magana da yawunsa, Yusuf Gusau, Channels TV ta ruwaito.

Matawalle ya bayyana cewa dakatarwar da aka yiwa wani hakimi a masarautar Shinkafi kwanan nan saboda hada kai da 'yan bindiga yana daya daga cikin sabbin matakan da ya yanke shawarar aiwatarwa.

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa ta fayyace banbanci tsakanin batun Minista Pantami da Adeosun

Cikin kwanaki 4 ku mika wuya ko ku fuskanci fushin gwamnati, Matawalle ga 'yan bindiga
Cikin kwanaki 4 ku mika wuya ko ku fuskanci fushin gwamnati, Matawalle ga 'yan bindiga Hoto: desertherald.com
Asali: UGC

Ya sha alwashin cewa nan da kwanaki hudu masu zuwa, zai shawo kan matsalar 'yan bindiga da ke damun mazauna a jihar.

Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana cewa ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugabannin hafsoshin kasar game da sabon salon da yake bi wajen samar da tsaro.

Ya ce, za a magance masu yaudarar da suka yi tuban muzuru tare da daukar sabbin matakaai.

A 'yan kwanakin nan, 'yan bindiga dauke da makamai sun mamaye jihar Zamfara yayin da 'yan bindiga suka kashe mazauna da dama a cikin mako guda.

Yawancin mazauna yankin sun tsere bayan ta'addancin da 'yan bindigan suka yi a fadin jihar.

Kashe-kashen sun yawaita, lamarin da ya sa Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar da martani.

KU KARANTA: EFCC Ta Kwamushe Wani Dan Kasuwa Mai Hada-Hadar Bitcoin Bayan Haramtata

A wani labarin daban, Shahararren mai fashin baki kan al'amuran yau da kullun, Shehu Sani, tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, ya bayyana irin tashin hankalin dake tattare da kashe-kashen da aka yi a Zamfara.

Tsohon sanatan ya nuna matukar damuwarsa ga yadda 'yan bindiga suka kashe akalla mazauna jihar 60 a cikin kwana daya kacal.

Sani, da yake kwatanta kididdigar abin da ake samu a wajen Najeriya, ya yi ikirarin cewa kisan da aka yi ya fi mummunan lamuran kisan da aka yi a Yemen da Afghanistan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.