Shehu Sani: Kashe-Kashen da Ake a Zamfara Yanzu Ya Fi Na Afghanistan
- Sanata Shehu Sani ya yi bayani game da hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa a jihar Zamafara
- Tsohon sanatan ya ce kashe-kashen da ake yi a jihar ta arewa ya zama abin kwatance a duniya
- Sani, a cikin wani sakon Twitter a ranar Alhamis, ya nuna juyayi ga wadanda lamarin ya shafa
Shahararren mai fashin baki kan al'amuran yau da kullun, Shehu Sani, tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, ya bayyana irin tashin hankalin dake tattare da kashe-kashen da aka yi a Zamfara.
Tsohon sanatan ya nuna matukar damuwarsa ga yadda 'yan bindiga suka kashe akalla mazauna jihar 60 a cikin kwana daya kacal.
Sani, da yake kwatanta kididdigar abin da ake samu a wajen Najeriya, ya yi ikirarin cewa kisan da aka yi ya fi mummunan lamuran kisan da aka yi a Yemen da Afghanistan.
KU KARANTA: Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da hedkwatar 'yan sandan jihar Delta
A kalamansa: "Mutane 60 da aka yiwa kisan gilla a cikin al'umomin Zamfara 13 a rana guda. Ko a Yemen ko Afghanistan irin wannan kisan gillar ba zai iya faruwa a 'yan kwanakin nan ba. Ina jajantawa dangin wadanda abin ya shafa."
Tun farko, Gwamna, Bello Matawalle a ranar Alhamis ya ba da umarnin rufe kasuwanni hudu ba tare da bata lokaci ba biyo bayan munanan kashe-kashen da suka faru.
KU KARANTA: Muna son ganin Buhari: Mata 'yan kasuwa sun koka kan tsadar abinci
A wani labarin, Kasar Amurka ta fitar da wata sabuwar takardar shawara game da tafiye-tafiye, tana mai gargadin ‘yan kasarta da kada su tafi jihohi 14 cikin 36 da ke Najeriya saboda matsalolin tsaro daban-daban.
Sanarwar shawarar tafiye-tafiyen da aka fitar a ranar Talata, 20 ga Afrilu, ta sanya Najeriya a kan Mataki na 3, wanda ke nuna cewa an shawarci ‘yan asalin Amurka da su sake tunani kafin tafiya zuwa Najeriya.
Takardar shawarar da Legit.ng ta gani a shafin yanar gizon gwamnatin Amurka ya sanya Najeriya a Mataki na 3 saboda aikata laifuka, ta'addanci, rikice-rikicen jama'a, satar mutane, da kuma aikata laifuka akan ruwa.
Asali: Legit.ng