Fadar shugaban kasa ta fayyace banbanci tsakanin batun Minista Pantami da Adeosun

Fadar shugaban kasa ta fayyace banbanci tsakanin batun Minista Pantami da Adeosun

- Fadar shugaban kasa ta bayyana banbanci tsakanin batun Minista Pantami da Adeosun

- Fadar ta ce batun Pantami da batu ne na takardun bogi da lamarin shugabanci ya sha bambam

- Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa ta goyi bayan Minista Pantami kan batun cece-kuce

Garba Shehu, hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, ya banbance tsakanin ikirarin da ake yi wa Dr Isa Ali Pantami da Kemi Adeosun, tsohuwar ministar kudi.

Shehu a ranar Juma’a, 23 ga Afrilu, ya bayyana cewa idan da Pantami yana da matsala game da jabun takardu, irin laifin da aka zargi Adeosun da shi, da fadar shugaban kasa ta dauki wani mataki a kansa.

Batun Adeosun ya zo ne lokacin da Channels TV ta tambayi hadimin na Shugaba Buhari kan dalilin da ya sa aka ce fadar Shugaban kasa ta yi saurin barin tsohuwar Ministar ta tafi amma ta zabi kare Pantami.

KU KARANTA: EFCC Ta Kwamushe Wani Dan Kasuwa Mai Hada-Hadar Bitcoin Bayan Haramtata

Fadar shugaban kasa ta fayyace banbanci tsakanin batun Minista Pantami da Adeosun
Fadar shugaban kasa ta fayyace banbanci tsakanin batun Minista Pantami da Adeosun Hoto: techeconomy.ng
Asali: UGC

Ya fayyace cewa a batun ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, tambaya ce ta bincika tunaninsa a lokacin da ya yi maganganun da ke cike da cece-kuce da nufin kokarin tabbatar da aniyarsa, in ji The Cable.

Shehu ya ce: “A yanayi na biyu wanda shi ne na Pantami, kuna binciken tunani ne, abinda ake kira‘ McCarthyism ’; kuna binciko hankulan mutane, ku fitar da abubuwan da suka fada, ko kuma za su fada, ko kuna tunanin za su fada, kuma su yi amfani da hakan a kansu,” inji shi.

"Da a ce Pantami ya kirkiri takardu na bogi kafin ya hau matsayinsa, halayya (ta shugabancin kasar) za ta sha bamban."

KU KARANTA: Najeriya Na Bukatar N1.89trn Don Yaki da Zazzabin Cizon Sauro, Amma Babu Kudi, Minista

A wani labarin, Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Isa Pantami, ya ce an yi kutse a shafinsa na Facebook amma yanzu an dawo da shi.

A ranar Litinin, Mista Pantami ya ruwaito cewa an yi kutse a shafinsa na sada zumunta. “An yi kutse a wannan asusun. Yanzu aka dawo dashi.

Ba Dr Isa Ali Pantami bane ke kula dashi, wasu matasa ne suke kulawa dashi. Ku yi watsi da duk wata bukata, tsokaci ko sako daga gare ta,” ya rubuta ta wannan shafin a daren Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel