Da duminsa: Mahaifiyar sarkin Kano, Maryam Bayero, ta rasu
- Maryam Bayero, mahaifiyar sarkin Kano Aminu Bayero ta rasu
- Marigayiyar ta amsa kiran mahaliccinta a yau Asabar, 24 ga watan Afrilu a wani asibitin Alkahira, Masar
- Wata majiya na iyalan ta tabbatar da mutuwar tata
Allah ya yi wa mahaifiyar Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, Hajiya Maryam Bayero rasuwa.
Marigayiyar, wacce ta kuma kasance uwa ga sarkin Bichi, Nasiru Bayero, ita ce matar marigayi Sarki Ado Bayero mafi tsufa da ke raye.
KU KARANTA KUMA: Gwamna El-Rufai ya samar da mafita ga hare-haren 'yan fashi a makarantu a Kaduna
KU KARANTA KUMA: Rayuwar kurkuku ta fiye mani, in ji Mallam Gambo wanda ya shafe shekaru 21 a gidan yari
Majiyoyi na iyalin sun tabbatar da mutuwar tata, inda suka ce ta mutu ne a safiyar ranar Asabar, 24 ga watan Afrilu a wani asibitin Alkahira, Masar, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
A gefe guda, mun ji cewa Allah ya yi wa Buhari Abubakar III, yayan Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar rasuwa, Daily Trust ta ruwaito.
Kafin rasuwarsa, Buhari ne ke rike da mukamin hakimin Sokoto ta Arewa.
Ya rasu ne a asibitin koyarwa ta Jami'ar Usmanu Danfodio da ke Sokoto bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
A wani labarin kuma, Hajiya Aishatu Ahmadu Bello, ta rasu ne a wani asibiti dake birnin Dubai, rahoton Daily Nigerian.
'Danta Hassan Danbaba ya tabbatar da labarin inda yace ta rasu bayan gajeruwar rashin lafiya.
Ya kara da cewa ana shirin dawo da gawarta Najeriya domin jana'iza.
Asali: Legit.ng