Da duminsa: Hajiya Aishatu, Diyar Sardaunan Sokoto Ahmadu Bello ta rasu

Da duminsa: Hajiya Aishatu, Diyar Sardaunan Sokoto Ahmadu Bello ta rasu

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa Allah ya yiwa mahaifiyar Magajin garin Sokoto, kuma 'diya ga Marigayi Sardaunan Sokoto, Sir Ahmadu Bello, rasuwa.

Hajiya Aishatu Ahmadu Bello, ta rasu ne a wani asibiti dake birnin Dubai, rahoton Daily Nigerian.

'Danta Hassan Danbaba ya tabbatar da labarin inda yace ta rasu bayan gajeruwar rashin lafiya.

Ya kara da cewa ana shirin dawo da gawarta Najeriya domin jana'iza.

Marigayiyar ta kasance uwargida ga marigayi Marafan Sokoto, Ahmad Danbaba.

KU KARANTA: Babu kasar da aka fi Najeriya yawan mutane marasa wutan lantarki, Bankin Duniya

Da duminsa: Hijya Aishatu, Diyar Sardaunan Sokoto Ahmadu Bello ta rasu
Da duminsa: Hijya Aishatu, Diyar Sardaunan Sokoto Ahmadu Bello ta rasu
Asali: Original

DUBA NAN: Dalilin da ya sa na daina sulhu da yan bindiga, Sheikh Ahmad Gumi

Duk a yau, Allah ya yi wa Buhari Abubakar III, yayan Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar rasuwa, Daily Trust ta ruwaito.

Kafin rasuwarsa, Buhari ne ke rike da mukamin hakimin Sokoto ta Arewa

Ya rasu ne a asibitin koyarwa ta Jami'ar Usmanu Danfodio da ke Sokoto bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel