Gwamna El-Rufai ya samar da mafita ga hare-haren 'yan fashi a makarantu a Kaduna

Gwamna El-Rufai ya samar da mafita ga hare-haren 'yan fashi a makarantu a Kaduna

- Nan ba da dadewa ba, gwamnati na iya fara gina makarantu kusa da barikin sojoji a Kaduna, idan za a iya amincewa da ra'ayin El-Rufai

- Gwamnan jihar Kaduna ya ce wannan zai taimaka wajen magance matsalar hare-hare a kan makarantu

- A halin yanzu, ya kuma yi kira da a samar da tsaro mai kyau a wuraren karatu

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai, ya bayyana abin da gwamnati za ta yi don dakatar da kai hare-hare a kan makarantu a fadin jihar.

A cewarsa, akwai bukatar gina makarantu kusa da sansanonin soji, jaridar The Cable ta ruwaito.

Ya bayyana hakan ne da yake magana yayin wani shiri a Gidan Talabijin na Najeriya (NTA) a ranar Juma'a, Afrilu 23.

Gwamna El-Rufai ya samar da mafita ga hare-haren 'yan fashi a makarantu a Kaduna
Gwamna El-Rufai ya samar da mafita ga hare-haren 'yan fashi a makarantu a Kaduna Hoto: @elrufai
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Rayuwar kurkuku ta fiye mani, in ji Mallam Gambo wanda ya shafe shekaru 21 a gidan yari

Ya ce za a iya dakile hare-haren da 'yan fashi ke kaiwa idan sojoji za su iya zuwa makarantar da abin ya shafa cikin minti 30.

Da yake ci gaba, ya bayyana cewa akwai bukatar jihar ta samu karin dakaru. Ya ce halin da ake ciki ya rataya a wuyan 'yan sanda da jami'an tsaron farin kaya da na NSCDC.

Ya ce:

“Na uku shi ne duba makarantu da kuma tabbatar da cewa sun kasance ba su fi nisan minti 30 daga wuraren girke sojoji ba, saboda abin da muke fuskanta tare da‘ yan fashin ya wuce karfin tsaron farar hula da ‘yan sanda. Muna buƙatar sojoji, sojojin sama da sojojin ruwa na musamman.

“Mun yi la’akari da yadda ake satar mutane a Kaduna da Zamfara, kuma mun cimma matsaya tare da sojoji cewa idan sojoji, na sama da na ruwa na musamman za su iya zuwa inda makarantun suke a cikin minti 30, ana iya dakile ayyukan ‘yan fashin.

“Wani abin da muka lura da shi shine cewa, wadannan‘ yan fashi suna kai hari makarantun karkara. Sau da yawa suna aiki da dare kuma sun fi son makarantun kwana. Saboda haka, hakan ya rage yawan makarantun da za mu kare.”

KU KARANTA KUMA: 2023: Faston Najeriya ya bayar da bayani kan wanda zai gaji Buhari

A wani labarin, sabon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Ahmed Musa a jiya Alhamis, ya bayar da gudummawar naira miliyan biyu ga makarantar sakandare ta sojoji ta Bukavu da ke Kano don gina masallaci.

Kyaftin din na Super Eagles ya bayar da gudummawar ne lokacin da ya ziyarci makarantar bayan kammala atisayen ranar Alhamis.

Ya kuma yi alkawarin samar da kayan kujeru a wasu daga cikin azuzuwan domin magance matsalar karancin kujeru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel