Yanzu-Yanzu: Allah Ya Yi Wa Yayan Sarkin Musulmi Rasuwa

Yanzu-Yanzu: Allah Ya Yi Wa Yayan Sarkin Musulmi Rasuwa

- Sarkin Musulmi Sultan Sa'ad Abubakar ya rasa yayansa Buhari Abubakar III

- Buhari Abubakar ya rasu ne a asibiti a garin Sokoto bayan fama da gajeruwa rashin lafiya

- Kafin rasuwar marigayin, shine hakimin Sokoto ta Arewa

Allah ya yi wa Buhari Abubakar III, yayan Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar rasuwa, Daily Trust ta ruwaito.

Kafin rasuwarsa, Buhari ne ke rike da mukamin hakimin Sokoto ta Arewa.

DUBA WANNAN: Ra'ayinsa kawai ya faɗa, DSS ta yi watsi da furucin DG a kan Pantami

Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa yayan Sarkin Musulmi rasuwa
Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa yayan Sarkin Musulmi rasuwa
Asali: Original

Ya rasu ne a asibitin koyarwa ta Jami'ar Usmanu Danfodio da ke Sokoto bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

KU KARANTA: El-Rufai Ya Lissafa Abubuwa 3 da Za a Yi Don Hana Ƴan Bindiga Satar Ɗalibai a Kaduna

Ku saurari karin bayani ...

A wani labarin daban, kun ji cewa an naɗa kakakin majalisar wakilan tarayyar Nigeria, Femi Gbajabiamila da Sanatoci uku da ke wakiltar Legas a matsayin mambobin Kwamitin bawa gwamna shawarwari wato GAC.

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, reshen jihar Legas ne ta bada sanarwar a ranar Laraba, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sanatoci ukun sune maiɗakin jagorar jam'iyyar APC na ƙasa, Oluremi Tinubu, Solomon Adeola da Tokunbo Abiru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel