Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da hedkwatar 'yan sandan jihar Delta

Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da hedkwatar 'yan sandan jihar Delta

- Gobara ta kame wani yankin hedkwatar 'yan sanda ta jihar Delta da tsakar ranan yau Alhamis

- Ba a samu rasa rai ko rauni ba, kuma an yi nasarar kashe gobarar cikin kankanin lokaci in ji hukumar

- An ruwaito cewa, hukumar ta yi gargadi kan yada jita-jita da ba ta da makama sabanin sanarwarsu

Hedikwatar ‘yan sanda ta Jihar Delta, Asaba, ta kone kurmus a ranar Alhamis yayin da jami’an ‘yan sanda da maziyarta suka bazama domin kare lafiyarsu.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa lamarin ya faru ne sakamakon tartsatsin wutar lantarkin da ya faru a dakin injin sarrafawa, wanda ya haifar da illa ga wasu na'urori da wani bangare na ginin, musamman rufin.

Ko da yake, ba a san musabbabin tartsatsin ba a lokacin hada wannan rahoto, amma wata majiya ta ce wasu jaruman ’yan sandan sun yi kokarin kubutar da wasu muhimman takardu daga bangaren da sauran ofisoshin da ke kusa da ginin.

KU KARANTA: Kaduna da jerin jihohi 13 da Amurka ta hana 'yan kasarta zuwa saboda tsaro

Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da hedkwatar 'yan sandan jihar Delta
Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da hedkwatar 'yan sandan jihar Delta Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Majiyar da ta nemi a sakaya sunan ta, ta ce, jami’an hukumar kashe gobara sun shigo cikin gaggawa da aka sanar da su su kashe wutar.

Da yake cewa ba a rasa rai ba, majiyar ta ce tuni aka koma kamar yadda aka saba.

Mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, PPRO, DSP Bright Edafe a cikin wata sanarwa da ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce; “A yau 22 ga Afrilu 2021, da misalin awanni 1445, an sami tashin gobara a dakin injin sarrafawa na hukumar.

“Rundunar 'yan sanda tana son bayyana cewa, gobarar ta shafi wani bangare ne kawai na dakin da ake kula da shi. An kira hukumar kashe gobara nan da nan, kuma isowarsu kan lokaci ya ceci halin da ake ciki.

“A yanzu haka an kashe wutar. Dalilin tashin gobarar ba a san shi ba tukuna amma ana tsammanin sakamakon wutar lantarki ne daga dakin injin sadarwa.

“A halin yanzu an fara bincike kan lamarin. Kwamishinan ‘yan sanda ya bukaci jama’a da su yi watsi da duk wani jita-jita sabanin gaskiyar da aka fada a sama”.

KU KARANTA: Muna son ganin Buhari: Mata 'yan kasuwa sun koka kan tsadar

A wani labarin, 'Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu ma'aikatan gini a wani yankin jihar Ondo a ranar Talata da ta gabata.

Wadanda lamarin ya rutsa da su na daga cikin wadanda ke aikin gyara yankin Ikaram/kunnu -Akoko na kananan hukumomin Akoko ta Arewa maso Yamma da kuma Arewa maso Gabas.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda reshen jihar Ondo, DSP Tee-Leo Ikoro ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels ta wayar tarho a ranar Laraba, sannan ya kara da cewa an sace ma’aikatan ne a ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: