Kaduna da jerin jihohi 13 da Amurka ta hana 'yan kasarta zuwa saboda tsaro

Kaduna da jerin jihohi 13 da Amurka ta hana 'yan kasarta zuwa saboda tsaro

- Kasar Amurka ta shawarci ‘yan kasarta da su sake tunani kafin tafiya zuwa Najeriya saboda matsalolin tsaro

- Gwamnatin Amurka ta lissafa jihohi 14 a Najeriya inda ya kamata ‘yan kasarta su guji zuwa idan har ma dole sai sun je kasar

- Borno, Yobe, Bayelsa, Cross River, Delta da kuma wasu jihohi tara an sanya su cikin jerin inda ake da matsalolin tsaro daban-daban

Kasar Amurka ta fitar da wata sabuwar takardar shawara game da tafiye-tafiye, tana mai gargadin ‘yan kasarta da kada su tafi jihohi 14 cikin 36 da ke Najeriya saboda matsalolin tsaro daban-daban.

Sanarwar shawarar tafiye-tafiyen da aka fitar a ranar Talata, 20 ga Afrilu, ta sanya Najeriya a kan Mataki na 3, wanda ke nuna cewa an shawarci ‘yan asalin Amurka da su sake tunani kafin tafiya zuwa Najeriya.

Takardar shawarar da Legit.ng ta gani a shafin yanar gizon gwamnatin Amurka ya sanya Najeriya a Mataki na 3 saboda aikata laifuka, ta'addanci, rikice-rikicen jama'a, satar mutane, da kuma aikata laifuka akan ruwa.

KU KARANTA: APC ta ce ba a taba yin gwamnati mai adalci irin ta Buhari ba a tarihin Najeriya

Kaduna da jerin jihohi 13 da Amurka ta hana 'yan kasarta zuwa saboda tsaro
Kaduna da jerin jihohi 13 da Amurka ta hana 'yan kasarta zuwa saboda tsaro Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sanarwar ta kara da cewa wasu yankunan sun fi wasu hadari. Ta ci gaba da jera matsalolin tsaro da suka shafi dukkan jihohi 14 da aka shawarci 'yan Amurka da su guji zuwa.

Ta’addanci da Satar Mutane

1. Borno

2. Yobe

3. Adamawa (bangaren arewa)

Satar Mutane

4. Bauchi

5. Gombe

6. Kaduna

7. Kano

8. Katsina

9. Zamfara

Badakala, Satar Mutane, da Aikata Laifuka a kan Teku

10. Akwa Ibom

11. Bayelsa

12. Kuros Riba

13. Delta

14. Ribas (banda Fatakwal)

Sanarwar ta ci gaba da nuna cewa Cibiyoyin Kula da Rigakafin Cututtuka (CDC) sun ba da sanarwar Kula da Kiwon Lafiya ta Mataki Na 1 ga Najeriya saboda Korona.

Sanarwar kiwon lafiya ta Mataki na 1 tana nuna karancin adadi na Korona a Najeriya.

KU KARANTA: Munason ganin Buhari: Mata 'yan kasuwa sun koka kan tsadar abinci

A wani labarin, 'Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu ma'aikatan gini a wani yankin jihar Ondo a ranar Talata da ta gabata.

Wadanda lamarin ya rutsa da su na daga cikin wadanda ke aikin gyara yankin Ikaram/kunnu -Akoko na kananan hukumomin Akoko ta Arewa maso Yamma da kuma Arewa maso Gabas.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda reshen jihar Ondo, DSP Tee-Leo Ikoro ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels ta wayar tarho a ranar Laraba, sannan ya kara da cewa an sace ma’aikatan ne a ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel