'Yan bindiga: Matawalle ya koka, ya ba da umarnin rufe kasuwannin Zamfara 4 nan take

'Yan bindiga: Matawalle ya koka, ya ba da umarnin rufe kasuwannin Zamfara 4 nan take

- Gwamnatin jihar Zamfara ta dauki wani muhimmin mataki domin dakile yawan kashe-kashen da 'yan fashi ke yi

- Gwamna Bello Matawalle ya rufe kasuwanni hudu na dan wani lokaci a kananan hukumomi uku

- Gwamnan ya bayyana ayyukan barnar da miyagu ke yi a matsayin rashin tunani da rashin tausayi

Biyo bayan harin da 'yan bindiga suka kaiwa mazauna Zamfara, Gwamna, Bello Matawalle a ranar Alhamis, 23 ga Afrilu, ya ba da umarnin rufe kasuwanni hudu nan take.

A wata sanarwa da ofishin gwamnan ya fitar abun ya shafi kasuwanni irin kasuwar Dansadau a karamar hukumar Maru, kasuwar Dauran a karamar hukumar Zurmi, TVC News ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Fadar shugaban kasa ta bayyana goyon bayanta ga Pantami

'Yan bindiga: Matawalle ya koka, ya ba da umarnin rufe kasuwannin Zamfara 4 nan take
'Yan bindiga: Matawalle ya koka, ya ba da umarnin rufe kasuwannin Zamfara 4 nan take Hoto: @Bellomatawalle1
Asali: Twitter

Sauran sune Kasuwannin Magami da Wanke a karamar hukumar Gusau da ke jihar.

Da yake magana kan lamarin a matsayin rashin imani, Matawalle ya nuna damuwa game da mummunan halin da yan ta’addan suka haifar.

Gwamnan, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, ya koka:

“Abin bakin ciki ne da Allah wadai ta’addancin da aka kaddamar a kan al’umma masu bin doka wadanda ke ba da gudummawa ga ci gaba musamman a jihar da kasa baki daya.

"Mu a matsayinmu na gwamnati mun damu da kashe-kashen rashin hankali, nakasawa da lalata rayuka da dukiyoyin galibi na garuruwan manoma."

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kashe basarake da wasu mutum uku a jihar Binuwai

A baya mun ji cewa wasu mutane da ake zargin 'yan fashi da makami ne sun jefa jihar Zamfara cikin jimami da juyayi bayan da suka kaddamar da hare-hare a garuruwa shida a ranar Laraba, 21 ga Afrilu, inda suka kashe akalla mutane 45.

A cewar jaridar Daily Trust, mutane da dama da suka hada da mata da yara sun bata a sanadiyyar hare-haren.

Legit.ng ta tattaro cewa yan fashin sun kuma lalata shaguna da gine-ginen gwamnati da masu zaman kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel