Yanzu Yanzu: Fadar shugaban kasa ta bayyana goyon bayanta ga Pantami

Yanzu Yanzu: Fadar shugaban kasa ta bayyana goyon bayanta ga Pantami

- Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Isa Pantami, ya sha suka kan maganganun da yayi wadanda ke cike da rudani

- ‘Yan Najeriya sun yi kira ga ministan da ya yi murabus daga mukaminsa ko kuma gwamnatin tarayya ta tsige shi

- Sai dai kuma fadar shugaban kasa ta kare Pantami, tana mai cewa wadanda ke neman a tsige shi ne ke ingiza kiraye-kirayen murabus din sa

Daga karshe fadar shugaban kasar Najeriya ta mayar da martani game da zargin cewa ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Pantami, ya yi kalamai a baya yana mai goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'adda.

anin fadar shugaban kasar na kunshe ne a cikin jerin sakwannin da babban mai taimakawa shuaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar a Twitter.

Shehu a cikin jawabin nasa a ranar Alhamis, 22 ga Afrilu, ya kare ministan tare da gabatar da cewa Pantami ya ce akwai kuruciya tare da shi a lokacin da yayi wadannan kalaman.

Yanzu Yanzu: Fadar shugaban kasa ta bayyana goyon bayanta ga Pantami
Yanzu Yanzu: Fadar shugaban kasa ta bayyana goyon bayanta ga Pantami Hoto: @DrIsaPantami
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Shugaban Amurka Joe Biden na tattaunawa da Buhari da sauran shugabannin duniya

A cewar kakakin shugaban kasar, a halin yanzu Pantami na fuskantar tirjiya wanda wasu da ke neman a tsige shi daga matsayin minista suka ingiza.

Ya ci gaba da cewa lokaci ya wuce, kuma tunannin ministan ya canza.

Ya ce abun bakin ciki ne yadda a yau ake yiwa shugabannin siyasa da na addini da na kungiyoyin fararen hula shagube dangane da kalamun da suka yi a baya koda sun yi watsi da su.

Har ila yau ya ce irin hakan kan shafi rayuwa da harkokin irin wadannan mutane ba tare da la’akari da lokacin da suka yi su ba.

Yayin da take nuna goyon bayanta ga ministan da ke cikin rudani, fadar shugaban kasa ta bayyana nasarorin da Pantami ya samu a wannan gwamnati mai ci.

Ya ce:

"A yau, akwai wani sabon salon yiwa shugabannin siyasa da na addini da na kungiyoyin fararen hula shagube dangane da kalamun da suka yi a baya – komai dadewa, har ma bayan sun yi watsi da su.

"Irin wannan lamarin kan shafi rayuwa da harkokin wadannan mutane kan abunda suka fadi, ba tare da la’akari da lokacin da suka yi su ba.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kashe basarake da wasu mutum uku a jihar Binuwai

"Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani,@DrIsaPantami yana fuskantar irin wannan kamfen din a halin yanzu, inda masu neman a cire shi daga mukaminsa suke zuga lamarin.

"Ba su damu da abin da ya fadi ko bai faɗi ba shekaru 20 da suka gabata: wannan shine kawai makamin da suke amfani da shi don ganin a raba shi da mukaminsa. Amma za su ci riba idan aka dakatar da shi daga yanke shawara da zai inganta rayuwar ‘yan Najeriya na yau da kullun.

"Ministan ya nemi gafara game da abin da ya fada a farkon 2000. Ba a yarda da ra'ayoyin ba a lokacin, kuma ba zai zama abun yarda ba a yau, idan da zai maimaita su.

"Amma ba zai sake maimaita su ba - don ya fito fili ya yi tir da maganganun da ya yi a baya a matsayin kuskure."

A gefe guda, Shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, ya musanta cewa ya yi fatali da yunkurin kiran a sauke Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami.

Jaridar The Cable ta rahoto Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya na cewa bai dakatar da Honarabul Ndudi Elumelu lokacin da ya bijiro da maganar ba.

Da yake karin-haske a ranar Alhamis, Femi Gbajabiamila, ya ce abin da ya faru shi ne ya ci gyaran Tony Elumelu na kawo batun ba tare da bin ka’ida ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel