An kashe mutum 45, da dama sun bata yayinda yan bindiga suka kai mamaya garuruwan Zamfara 6

An kashe mutum 45, da dama sun bata yayinda yan bindiga suka kai mamaya garuruwan Zamfara 6

- Wasu al'ummomin jihar Zamfara na kirga asarar da suka yi bayan wasu 'yan bindiga sun far masu a ranar Laraba, 21 ga Afrilu

- An tattaro cewa hare-haren ya yi sanadiyar rasa rayukan a kalla mutane 45 yayin da har yanzu ba a san inda wasu da yawa suke ba

- Rahotanni sun ce ‘yan fashin sun kona gidaje da shaguna da dama

Wasu mutane da ake zargin 'yan fashi da makami ne sun jefa jihar Zamfara cikin jimami da juyayi bayan da suka kaddamar da hare-hare a garuruwa shida a ranar Laraba, 21 ga Afrilu, inda suka kashe akalla mutane 45.

A cewar jaridar Daily Trust, mutane da dama da suka hada da mata da yara sun bata a sanadiyyar hare-haren.

Legit.ng ta tattaro cewa yan fashin sun kuma lalata shaguna da gine-ginen gwamnati da masu zaman kansu.

An kashe mutum 45, da dama sun bata yayinda yan bindiga suka kai mamaya garuruwan Zamfara 6
An kashe mutum 45, da dama sun bata yayinda yan bindiga suka kai mamaya garuruwan Zamfara 6 Hoto: @Bellomatawalle1
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Jerin sunaye: Babban ibtila’i ya afkawa APC yayin da shugabannin jam'iyyar 5 suka Mutu Ba zato ba tsammani

Garuruwan da abin ya shafa suna cikin Gundumar Magami da ke karamar hukumar Gusau, wato; Yar Doka, Kango, Ruwan Dawa, Madaba, Arzikin Da da Mairairai.

An ambaci mazauna suna cewa maharan dauke da makamai sun fara kai mamaya kauyen 'Yar Doka a kan babura sannan suka harbe duk wanda suka gani.

Daya daga cikin mutanen da suka firgita ya ce har yanzu ba a san inda mutane da dama suke ba bayan sun tsere daga harin.

An gano cewa 'yan bindigar sun tafi wani kauye mai suna Kango kuma suka harbe akalla mutane 11.

Wani mazaunin, Halliru Bala, ya ce maharan sun kashe mutane 13 a Ruwan Dawa da ke kan hanyar Gusau-Dansadau.

An nakalto Bala yana cewa:

“Sun kuma harbe mutane bakwai a Madaba, biyu a Mairairai sannan mutum biyar a al’umman Arzikin Da.

"A yanzu haka da nake magana da ku, an riga an kawo gawarwakin mutanen bakwai da aka kashe zuwa garin Magami kuma za a yi jana'izar su yau da yamma bayan an yi buda baki."

Bala ya ce akasarin wadanda suka mutu wadanda suka tafi ne don ba da taimako ga garuruwan da ake kai wa hari.

BBC Hausa ta sanya adadin wadanda suka rasa rayukansu sama da 50 a rahotonta na abin da ya faru.

KU KARANTA KUMA: Gobara ta tashi a zauren majalisar dokokin jihar Katsina

'Yan sandan jihar ta yi gum

Daily Trust ta bayyana cewa har yanzu rundunar ‘yan sanda a jihar Zamfara ba ta amsa bukatarta ba don tabbatar da ci gaban.

Jaridar ta kara da cewa kiraye-kirayen da aka yi wa kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Abubakar Dauran, a daren Laraba ba a amsa ba.

A wani labarin, Shugaban Hafsoshin Soji, Laftanan Janar Ibrahim Attahiru, ya bayyanawa majalisar dattawa cewa a kara musu kudi don siyan makamai da kayan yaki.

Attahiru, ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayinda ya karbi bakuncin kwamitin majalisar dattawa kan hukumar Soji a ofishinsa dake birnin tarayya Abuja, rahoton TheCable.

Ya ce hukumar na bukatar goyon bayan kwamitin don kawar da dukkan matsalolin tsaron kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel