Yan bindiga sun kashe basarake da wasu mutum uku a jihar Binuwai

Yan bindiga sun kashe basarake da wasu mutum uku a jihar Binuwai

- Yan bindiga sun kashe wani basarake, Cif Hyacinth Ajon da wasu mutane uku a wasu hare-hare daban a Karamar Hukumar biyu ta Jihar Benuwai

- Lamarin ya afku ne a ranar Laraba, 21 ga watan Afrilu

- Sai dai kuma ana zargin makiyaya da alhakin kisan mamatan

Wasu ‘yan bindiga a ranar Laraba sun kashe wani basarake, Cif Hyacinth Ajon da wasu mutane uku a wasu hare-hare daban a Karamar Hukumar biyu ta Jihar Benuwai.

An kashe marigayin basaraken tare da wani, Benjamin Anakula a garin Tse Zoola na karamar hukumar Makurdi yayin da aka kashe wasu mutane biyu da ba a fadi sunayensu ba a yankin Guma na jihar.

KU KARANTA KUMA: Hotuna da bidiyon kasaitaccen bikin mutuwar aure da wata yar Najeriya tayi

Yan bindiga sun kashe basarake da wasu mutum uku a jihar Binuwai
Yan bindiga sun kashe basarake da wasu mutum uku a jihar Binuwai Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

Babban dattijo a yankin, Aho Zoola, ya yi zargin cewa wasu ‘yan bindiga da ake zaton makiyaya ne sun far wa mazauna kauyen da misalin karfe 2:00am, suka yi ta harbi ba kakkautawa sannan suka kashe mutanen biyu.

Zoola a cewar rahoton daya daga cikin hadiman gwamna Samuel Ortom a kafafen yada labarai, ya bayyana cewa harin da aka kai wa yankinsu na kakkara ya zo masu da mamaki domin ba su taba samun wata matsala da makiyaya ba.

Hadimin gwamnan, Jimmin Geoffrey, ya bayyana cewa gwamnan yana dawowa daga wani jana’iza a yankin lokacin da ya tsaya domin yin jaje ga mazauna kauyukan wadanda tuni suka kaura daga gidajensu.

Gwamnan ya kuma ba su tabbacin cewa zai yi duk mai yiwuwa don ganin an samu hukumomin tsaro a yankin.

Hakazalika, Shugaban karamar hukumar Guma, Caleb Aba, ya shaida wa manema labarai a Makurdi ta wayar tarho cewa an kashe sauran mutanen biyu a ranar Laraba a yankin Mbayer-Yandev na yankin Guma.

KU KARANTA KUMA: Muna son ganin Buhari: Mata 'yan kasuwa sun koka kan tsadar abinci

Sai dai kuma Aba ya zargi makiyaya da aiwatar da kisan a yankin sa.

A gefe guda, wasu mutane da ake zargin 'yan fashi da makami ne sun jefa jihar Zamfara cikin jimami da juyayi bayan da suka kaddamar da hare-hare a garuruwa shida a ranar Laraba, 21 ga Afrilu, inda suka kashe akalla mutane 45.

A cewar jaridar Daily Trust, mutane da dama da suka hada da mata da yara sun bata a sanadiyyar hare-haren.

Legit.ng ta tattaro cewa yan fashin sun kuma lalata shaguna da gine-ginen gwamnati da masu zaman kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel