Shugaban Amurka Joe Biden na tattaunawa da Buhari da sauran shugabannin duniya
Shugaban Amurka, Joe Biden, ya gayyaci Muhammadu Buhari da sauran shugabannin duniya 39 zuwa taron koli kan canjin yanayi.
Fadar White House a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa taron kwanaki biyu da za a fara ranar Alhamis, 22 ga Afrilu, an shirya shi ne da nufin jan hankalin kasashe don su kara kaimi wajen yaki da canjin yanayi kafin lokaci ya kure.
Har ila yau, manyan jami’ai, shugabannin kamfanoni, da manyan mutane a duniya kamar Paparoma Francis da mai taimakon jama'a, Bill Gates, wadanda aka shirya za su gabatar da jawabai, sun halarci taron.
KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kashe basarake da wasu mutum uku a jihar Binuwai
Ga jerin sunayen shugabannin duniya da ke halartar taron:
1. Shugaba Muhammadu Buhari, Najeriya
2. Firayim Minista Gaston Browne, Antigua da Barbuda
3. Shugaba Alberto Fernandez, Ajantina
4. Firayim Minista Scott Morrison, Ostiraliya
5. Firayim Minista Sheikh Hasina, Bangladesh
6. Firayim Minista Lotay Tshering, Bhutan
7. Shugaba Jair Bolsonaro, Brazil
8. Firayim Minista Justin Trudeau, Kanada
9. Shugaba Sebastián Piñera, Chile
10. Shugaba Xi Jinping, Jamhuriyar Jama'ar Sin
11. Shugaba Iván Duque Márquez, Colombia
12. Shugaba Félix Tshisekedi, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo
13. Firayim Minista Mette Frederiksen, Denmark
14. Shugaba Ursula von der Leyen, Hukumar Tarayyar Turai
15. Shugaba Charles Michel, Majalisar Turai
16. Shugaba Emmanuel Macron, Faransa
17. Shugaba Ali Bongo Ondimba, Gabon
18. Shugabar gwamnati Angela Merkel, Jamus
19. Firayim Minista Narendra Modi, Indiya
20. Shugaba Joko Widodo, Indonesia
21. Firayim Minista Benjamin Netanyahu, Isra'ila
22. Firayim Minista Mario Draghi, Italiya
23. Firayim Minista Andrew Holness, Jamaica
24. Firayim Minista Yoshihide Suga, Japan
25. Shugaba Uhuru Kenyatta, Kenya
26. Shugaba David Kabua, Jamhuriyar Tsibirin Marshall
27. Shugaba Andrés Manuel López Obrador, Mexico
28. Firayim Minista Jacinda Ardern, New Zealand
29 Firayim Minista Erna Solberg, Norway
30. Shugaba Andrzej Duda, Poland
31. Shugaba Moon Jae-in, Jamhuriyar Koriya
KU KARANTA KUMA: Hotuna da bidiyon kasaitaccen bikin mutuwar aure da wata yar Najeriya tayi
32. Shugaba Vladimir Putin, Tarayyar Rasha
33. Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, Masarautar Saudi Arabiya
34. Firayim Minista Lee Hsien Loong, Singapore
35. Shugaba Matamela Cyril Ramaphosa, Afirka ta Kudu
36. Firayim Minista Pedro Sánchez, Spain
37. Shugaba Recep Tayyip Erdoğan, Turkiyya
38. Shugaba Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan, Hadaddiyar Daular Larabawa
39. Firayim Minista Boris Johnson, United Kingdom
40. Shugaba Nguyễn Phú Trɔng, Vietnam
A wani labarin, shugaba Muhammadu Buhari ya gana da kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya karkashin jagorancin gwamnan jihar Plateau, Simon Bako Lalong.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce anyi wannan zama ne ranar Alhamis a fadar shugaban kasa.
Daga cikin wadanda suka halarci zaman akwai gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle; gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal; da gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufa'i.
Asali: Legit.ng