Hotuna da bidiyon kasaitaccen bikin mutuwar aure da wata yar Najeriya tayi

Hotuna da bidiyon kasaitaccen bikin mutuwar aure da wata yar Najeriya tayi

- Wata yar Najeriya, Ikea Bello, ta yi fice a kafafen sada zumunta bayan ta yi wani abin da ba a saba gani ba

- Kwararriyar mai koyar da rayuwar ta yi bikin mutuwar aurenta cikin kasaita

- Ta yi gagarumin liyafa yayin da take murnar samun yancinta tare da abokai da masu fatan alheri

Mutane biyu kan kulla aure tare da fatan alkhairi amma rayuwa ta kan sauya abubuwa zuwa hanyar da ba a yi tsammani ba. Wannan shi ne lamarin wata likita yar Najeriya, Ikea Bello.

A kwanan nan ne Bello ta sanya ‘yan Najeriya a shafukan sada zumunta cikin al’ajabi bayan ta yi gagarumin biki don murnar rabuwa da mijinta.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar APC Kaduna ta kafa tarihi a Najeriya, ta gudanar da jarrabawa ga masu neman kujerun ciyamomi

Hotuna da bidiyon kasaitaccen bikin mutuwar aure da wata yar Najeriya tayi
Hotuna da bidiyon kasaitaccen bikin mutuwar aure da wata yar Najeriya tayi Hoto: @thewarriorwomanofficial
Asali: Instagram

A shafukan zumunta, ƙwararren mai horar da rayuwar ta wallafa hotuna da bidiyon kasaitaccen bikin.

Ya bayyana an zabi kalar suturar da za a sa ganin yadda kawayen matar suka sanya jajayen kaya. Ikea Bello kuma ta saka wata kayatacciyar karammiski mai kalar shuni da ja kuma an ganta tana shakatawa tare da baƙinta.

A cewarta, mutuwar aurenta da bikin 'yancin ya kasance abin birgewa. A cikin kalmomin ta, abun ya kayatar.

Bello ta yi shirya bikin kamar wani sabon bikin aure. Ta canza kayanta har ma ta bayyana cewa zabin kayan da tayi na farko ya samu karbuwa ne daga yar wasan Nollywood, Tonto Dikeh.

Duk da rashin bayyana ainahin abin da ya haifar da mutuwar auren nata, ta bar wasu alamu a cikin maudu’inta inda ta bayyana cewa ta rabu da mai yada jita-jita kuma cewa ta tsira daga zamantakewar mai guba.

Kalli hotuna daga wallafarta a kasa:

Hotuna da bidiyon kasaitaccen bikin mutuwar aure da wata yar Najeriya tayi
Hotuna da bidiyon kasaitaccen bikin mutuwar aure da wata yar Najeriya tayi Hoto: @thewarriorwomanofficial
Asali: Instagram

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An yi garkuwa da ma’aikatan jinya 2 da ke bakin aiki a Kaduna

Hotuna da bidiyon kasaitaccen bikin mutuwar aure da wata yar Najeriya tayi
Hotuna da bidiyon kasaitaccen bikin mutuwar aure da wata yar Najeriya tayi Hoto: @thewarriorwomanofficial
Asali: Instagram

A gefe guda, wasu ma'aurata 'yan Najeriya da aka ambata da suna Mista da Misis Ogeah suna murnar zuwan ‘yan ukunsu bayan shekaru 11 da aure da kuma bari da dama.

Wata 'yar uwarsu, Evelyn Odume, wacce ta ba da wannan labarin mai ban mamaki a ranar Lahadi, 11 ga Afrilu, ta bayyana cewa Allah ya ba shaidan kunya, Yabaleft ta ruwaito.

Shafin Twitter @Naija_PR ma ya yada labarin mai dadi a dandalin sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel