Maigida ta nemi na kwanta da ita a madadin biyan kuɗin haya, in ji Saurayi

Maigida ta nemi na kwanta da ita a madadin biyan kuɗin haya, in ji Saurayi

- Wani matashi ya bada labarin yadda matar mai gidan da ya ke haya ta nemi rika kwana da ita a madadin kudin haya

- Ya ce da farko bai amince ba amma daga bisani ya yarda saboda ta fada masa mijinta ba zai damu ba domin shima wasu matan ya ke nema

- Daga baya dai matashin ya yi nadama ya kuma ce ba zai cigaba da hakan ba amma kwatsam sai ya gano rasit din bogi ta bashi

Wani mutum dan Nigeria ya bada labarin yadda matar mai gidan da ya ke zaune yana haya ta nemi ya rika kwana da ita a madadin kudin haya da zai rika biya, The Nation ta ruwaito.

A cewar mutumin, ya shiga gidan hayar da ke unguwar Lekki a Legas shekaru biyu da suka gabata kuma matar mai gidan ita ce ta tarbe shi ta nuna masa cikin gidan da wasu abubuwa.

Maigida ta nemi na kwanta da ita a madadin biyan kuɗin haya, in ji Saurayi
Maigida ta nemi na kwanta da ita a madadin biyan kuɗin haya, in ji Saurayi. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kotun shari'a ta raba aure a Zamfara saboda tsabar girman mazakutar miji

Ta nuna masa alamun tana son sa tunda suka hadu da farko inda ta ce idan ya amince ba zai cigaba da biyan kudin haya ba. Duk da cewa da farko bai yarda ba, daga baya ya amince amma a karshe ya yi nadamar hakan.

"Saboda irin aikin da na ke yi, ina bukatar wurin zama mai walwala domin hakan zai taimaka min samun abokan hulda masu hannu da shuni. Kudin hayar da tsada har sai da na ci bashi kafin na samu kudin biyan gidan hayar," in ji shi.

Ya ce matar mai gidan hayar lauya ce sannan shekarunta sun kai 40. Ta kuma lura ba shi da aure hakan yasa ta rika bibiyarsa tun yana kaucewa har ya amince da ita.

"Ta fada min cewa mijinta ba shi da lokacin ta domin shima neman wasu matan ya ke yi a waje don haka sai naga tamkar ba wani abin damuwa bane domin shima yana hulda da wasu matan bayan ita," a cewarsa.

KU KARANTA: Jam'iyyar PDP da dakatar da Sanata Hayatu Gwarzo a Kano

"Bayan ta bani rasit din gidan hayar, sai na fada mata ba zan iya cigaba da abin da ke tsakaninmu ba. Bayan ta kwashi tsawon lokaci tana roko amma na ki yarda sai ta turo min sakon tes cewa in saurari abin da zai biyo baya.
"Kwatsam kawai sai naga notis cewa in biya kudin haya kuma an kara kudin hayar daga naira miliyan uku zuwa hudu, idan kuma ban biya cikin wata daya ba za a tashe ni. Nan take na sake duba rasit din da ta bani a baya sai na gano ashe na bogi ne.
"Na kira abokina lauya na fada masa abin da ya faru amma ya ce min babu abin da zan iya yi a kai sai dai in nemi kudin hayar in biya ko kuma in bar gidan ko kuma in amince da abin da matar mai gidan ke nema a gare ni.
"Na ji kamar in fallasa ta a dandalin sada zumunta sai dai hakan na nufin zan rasa gidan hayar da na ke ciki ga shi kuma harkokin kasuwancin ba su tafiya kamar yadda ake so. Ni dai na shiga uku kam," in ji shi.

A halin yanzu dai addu'a na ke yi Ubangiji ya fitar da ni daga wannan halin da na shiga.

A wani labarin daban kun ji cewa 'yan sanda a jihar Kano sun ceto wata yarinya mai shekaru 15, Aisha Jibrin, da iyayenta suka kulle ta a daki tsawon shekaru 10 a Darerewa Quaters a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel