Wadanda suka daliban Kaduna sun bukaci N800m matsayin kudin fansa

Wadanda suka daliban Kaduna sun bukaci N800m matsayin kudin fansa

- Karo na biyu, yan bindiga suka kuma awon gaba da dalibai a makarantar daba da sakandare

- Jami'an Gwamnatin jihar sun kai ziyara jami'ar don ganewa idanuwansu abinda ya faru

- Yan bindiga sun fara tuntuban iyayen daliban don bukatar kudin fansa

Yan bindigan da sukayi awon gaba da daliban jami'ar Greenfield a jihar Kaduna sun bukaci a basu kudi milyan 800 matsayin kudin fansa kafin su sake daliban.

A cewar rahoton TheNation, yan bindigan sun yi barazanar kashe daliban idan ba'a biya kudin ba.

Majiyoyi sun bayyana cewa adadin daliban da aka sace na tsakanin 17 da 23; kimanin mata 14 da maza takwa.

An samu labarin cewa yanzu haka an kaddamar da tattaunawa da su.

Wani dan'uwan daya daga cikin daliban da aka sace, Georgina Stephen, ya ce yan bindigan sun bukaci kudin fansa.

Wani mahaifin daya daga cikin daliban ya tabbatar da hakan, ya ce yan bindigan sun kira kuma sun bukaci kudin fansa.

KU DUBA: Rikicin PDP: Bangaren Kwankwaso sun dau fansa, an dakatar da Sanata Gwarzo

Wadanda suka sake daliban Kaduna sun bukaci N800m matsayin kudin fansa
Wadanda suka sake daliban Kaduna sun bukaci N800m matsayin kudin fansa Hoto: Jami'ar Greenfield
Asali: UGC

DUBA NAN: Munanan hare-hare, garkuwa da mutane, da kashe-kashe 6 da suka auku jiya Laraba

Jiya kun ji cewa wasu yan bindiga sun kai hari jami'ar Greenfield dake hanyar Abuja zuwa Kaduna da dare.

Hukumar yan sanda jihar Kaduna, ta tabbatar da labarin.

Hakazalika kwamishanan tsaro da harkokin cikin gidan jihar, Samuel Aruwan, ya bayyana cewa bayan sintiri da bibiyan sahun yan bindigan, an tabbatar da kisan daya daga cikin ma'aikatan jami'ar.

Ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Laraba a Facebook.

"Bayan bincike da sintiri, an tabbatar da kisan Paul Ude Okafor, wani ma'aikacin jami'ar, yayinda akayi awon gaba da dalibai," yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel