Nasara daga Allah: 'Yan sanda sun ragargaji 'yan bindiga a Zamfara, sun hallaka 30 har lahira
- 'Yan sanda a jihar Zamfara sun fatattaki 'yan bindiga sama a wani samame da suka kai a Zamfara
- Sun kuma fatattakesu tare da hallaka sama da 30 daga cikinsu, in da da dama suka fece zuwa daji
- Rahotanni sun bayyana cewa, a kasa da wata daya 'yan bindiga sun yi munanan barna a yankin arewa maso yammaci
'Yan sandan Najeriya sun hallaka 'yan bindiga 30 bayan da wasu gungun 'yan ta'adda suka afkawa kauyuka Hudu a arewa maso yammacin kasar, in ji 'yan sanda a ranar Talata.
Mai magana da yawun ‘yan sanda na jihar ta Zamfara Mohammed Shehu ya fada a cikin wata sanarwa cewa, akalla mazauna kauyuka 10 aka kashe a wasu hare-hare daban-daban, kafin 'yan sanda su mai da martani kan 'yan bindigan.
Wasu gungun 'yan ta'adda dauke da muggan makamai wadanda aka fi sani da "'Yan bindiga" sun zama manyan masu kalubalantar tsaro a arewa maso yammacin Najeriya, suna addabar kauyuka tare da yin garkuwa da mutane da dama tare da karbar kudin fansa.
KU KARANTA: Rikici ya barke bayan da Gwamnan PDP ya samu gayyatar ficewa zuwa APC
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, ‘yan sanda sun ce wasu 'yan bindiga sun kai samame a kauyukan Gobirawa, Gora, Rini da Madoti Dankule da ke jihar ta Zamfara a safiyar ranar Talata.
Sanarwar ta ce "A sakamakon arangamar, kimanin 'yan bindiga 30 an kashe su yayin da wasu suka tsere zuwa daji."
Kungiyoyin masu aikata laifuka a kwanan nan sun mai da hankalinsu ga satar dalibai da ‘yan makaranta don neman kudin fansa.
'Yan bindiga a watan da ya gabata sun kame dalibai 39 daga dakunan kwanan su da ke Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji ta Tarayya da ke Afaka a cikin jihar Kaduna, bayan artabu da sojoji.
An saki wasu daga cikin daliban, kuma wannan shi ne karo na hudu da aka yi garkuwa da dalibai a wata makaranta ko kwaleji a arewa maso yammacin Najeriya tun farkon shekarar 2021.
KU KARANTA: Buhari ya girgiza: Mutuwar Deby ta haifar da ‘Babban Gurbi’ a yaki da Boko Haram
A wani labarin, Tawagar 'yan sanda 144 daga Najeriya sun isa kasar Somaliya domin bunkasa ayyukan tabbatar da tsaro a kasar, in ji tawagar Tarayyar Afirka a ranar Lahadi. CGTN Africa ta ruwaito.
Mai kula da ayyukan ‘yan sanda na rundunar 'yan sanda Daniel Ali Gwambal ya ce za a tura jami’an ‘yan sanda 30 da za su yi aiki a karkashin AMISOM na tsawon shekara guda zuwa Beletweyne da ke cikin jihar HirShabelle.
Ya kuma bayyana cewa, sauran za su yi aiki a wurare daban-daban a Mogadishu, babban birnin kasar.
Asali: Legit.ng