Majalisar Dattawa na duba yiyuwar hanyar sanin yawan shanu da awakai a Najeriya

Majalisar Dattawa na duba yiyuwar hanyar sanin yawan shanu da awakai a Najeriya

- Majalisar Dattawa ta kasa ta zauna kan wani kudurin samar da rumbum adana bayanan shanu

- Kudurin an bayyana cewa, zai taimaka wajen kawo karshen yawaitar satar shanu a fadin kasar

- Hakazalika an ce, kudurin wani yunkuri ne na tsaftace harkar kiwo a kasar don inganta abinci

Majalisar dattijai na nazarin kudirin dokar da ke neman samar da rumbun adana bayanan shanu a duk fadin kasar, The Cable ta ruwaito.

Kudurin dokar da za a samar a Hukumar Kula da Kiwo ta Kasa ta zarce karatu na biyu a zaman majalisar na ranar Talata.

Dangane da dokar, wacce Muhammad Enagi daga Neja ta kudu ya bijiro da ita, hukumar za ta kasance mai kula da ganowa, bincikowa da kuma yin rajistar dabbobi kamar shanu da awaki da sauran abubuwa, da tunanin hakan zai hana satar shanu.

Hakan nan kuma za a tabbatar da kariya, lura da kula da dukkan dabbobi a Najeriya.

KU KARANTA: APC ta ce ba a taba yin gwamnati mai adalci irin ta Buhari ba a tarihin Najeriya

Majalisar Dattawa na duba yiyuwar hanyar sanin yawan shanu da awakai a Najeriya
Majalisar Dattawa na duba yiyuwar hanyar sanin yawan shanu da awakai a Najeriya Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

An gabatar da irin wannan kudurin a majalisar dattijan da ta gabata amma ba a zartar da shi ba.

Wasu daga cikin ayyukan ofishin da akeson kirkirar sun hada da: kirkirar rumbun adana bayanan dabbobi na kasa; kula da zirga-zirgar dabbobi da tabbatar da sarrafa su don hana barkewar cututtuka.

Hakanan ana tsammanin ta da tabbatar da lafiyar abinci, nuna gaskiya da bayanai a jerin kayan abinci, tare da hana satar shanu don kawo karshen rikicin manoma da makiyaya da ya dade yana addabar Najeriya.

Enagi ya ce baya ga duba satar shanu, kudirin zai taimaka wajen magance cututtuka da sauran barazana ga rayuwar dan adam sakamakon zirga-zirgar dabbobi.

Ya ce hukumar zata kula da aikin za kuma ta tabbatar da cewa ana shigo da kayayyakin dabbobi, ko kuma sayar da su a cikin Najeriya cikin rahusa don tabbatar da lafiyar dan adam.

Sanatan ya ce tantance dabbobi da hukumar za ta yi zai hada da mallakarsu da sauran bayanai ciki har da asalinsu, wurin haihuwarsu da jinsinsu.

Bayan tattaunawa kan kudirin, zauren ya mika shi ga kwamitinta kan harkokin noma da ci gaban karkara domin ci gaba da aiki akai.

KU KARANTA: An yi kutse a shafin Facebook na Dr Pantami biyo bayan wani sharhi da ya yi

A wani labarin, Gwamnatin jihar Ondo ta fada a ranar Lahadi cewa daga yanzu za ta yi gwanjon shanun da aka kama da lalata gonaki bayan samun umarnin kotu, yayin da za a hukunta masu shanun da aka kama, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kwamandan rundunar tsaro ta jihar ta Amotekun, Cif Adetunji Adeleye ne ya bayyana hakan yayin sanya hannu kan yarjejeniyar sakin shanu sama da 250 da Amotekun suka kama a Akure, babban birnin jihar.

A cewar kwamandan, Amotekun ta kame shanu sama da 250 a cikin jihar, biyo bayan kiraye-kirayen nuna damuwa da koke-koke da manoman yankin Ipogun, Ilara, Owena Dam a karamar hukumar Ifedore ta jihar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel