An yi kutse a shafin Facebook na Dr Pantami biyo bayan wani sharhi da ya yi
- Ministan Sadarwa Dr Pantami ya bayyana cewa, an yi kutse a shafinsa na Facebook ranar Litinin
- Amma ya sake bayyana cewa, shafinsa ya sake dawo hannunsa, wanda yanzu yake kula dashi
- Kutse a shafin ya biyo bayan wani sharhi da aka yi a Facebook din ta amfani da shafin nasa
Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Isa Pantami, ya ce an yi kutse a shafinsa na Facebook amma yanzu an dawo da shi.
A ranar Litinin, Mista Pantami ya ruwaito cewa an yi kutse a shafinsa na sada zumunta.
“An yi kutse a wannan asusun. Yanzu aka dawo dashi. Ba Dr Isa Ali Pantami bane ke kula dashi, wasu matasa ne suke kulawa dashi. Ku yi watsi da duk wata bukata, tsokaci ko sako daga gare ta,” ya rubuta ta wannan shafin a daren Litinin.
Wannan na zuwa ne bayan wani sharhi na tsinewa Deji Adeyanju, wani mai fafutuka, dake ta kiraye-kirayen murabus din ministan.
KU KARANTA: Tarihin Ibnu Battuta mai daukar hankali, daya daga cikin matafiyan da suka zagaye duniya
Mista Adeyanju ya rubuta wasika zuwa ofishin jakadancin Amurka da kuma na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) don bincikar zargin da ake yi wa malamin.
A karkashin wani sakon da ya wallafa a shafin Facebook wanda ke nuna Mista Adeyanju a matsayin makiyin Musulunci, Ministan ya rubuta da Hausa "Allah ya tsine masa albarika".
An share sharhin yanzu haka kuma baya bayyane a shafin.
Yayin da sakonsa na Facebook ya ce ministan ba shi ke kula da shafin ba, binciken da aka yi ya nuna cewa adireshin imel din da aka yi amfani da shi wajen bude shafin ”isapantami@yahoo.com” na Mista Pantami ne.
Adireshin imel "isaaliibrahim@hotmail.com" da aka bayar domin bincike shima mallakin ministan ne kuma ya bayyana a bayanansa a shafin yanar gizon NOUN.
Wata mai taimaka wa Ministan kan harkokin yada labarai, Uwa Suleiman, da ta karbi wani rubutu daga wakilin Premium Times, bata amsa tambayoyin jaridar ba.
KU KARANTA: Rikici ya barke bayan da Gwamnan PDP ya samu gayyatar ficewa zuwa APC
A wani labarin, Wani jigo a jam’iyyar APC, Cletus Obun, ya yi kira da a kori ko a tursasa murabus ga ministan yada sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Pantami.
Obun ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin, 19 ga Afrilu yayin da yake magana a wani shirin kumallo na gidan Talabijin mai zaman kansa na Afirka.
Ya bayyana cewa ya kamata a kori Dr Pantami daga mukamin sa idan har ba ya son yin murabus duba da abubuwan da aka bayyana game da shi.
Asali: Legit.ng