Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai hari ofishin yan sandan Enugu, an kashe jami’ai uku
- Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sake kai hari yankin kudu maso gabashin Najeriya
- A wannan karon jihar Enugu aka kai wa hare-hare bayan makamancin lamarin a jihohin da ke makwabtaka
- Rundunar ‘yan sanda ta Enugu ta tabbatar da harin, yayin da shaidun gani da ido suka ce mamayar ta dauki tsawon sa’a guda
Jaridar The Punch ta bada rahoton cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari wani ofishin yan sanda a Adani, karamar hukumar Uzo-Uwani na jihar Enugu a ranar Laraba, 21 ga watan Afrilu.
A cewar rahoton, an kashe ‘yan sanda uku da ke bakin aiki, yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harin.
KU KARANTA KUMA: Mata ta haifi yan uku bayan shekaru 11 da aure da yin bari sau 6
An gano cewa an lalata kayayyakin tsaro a ofishin.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da harin, ta bakin kakakinta, Daniel Ndukwe wanda ya ce za a samar da karin bayani nan gaba.
Harin da aka kaiwa ofishin ‘yan sanda ya fara ne da misalin karfe 2:30am kuma ya ci gaba har zuwa kusan 3:30am.
KU KARANTA KUMA: Rikita rikita: Wasa ya ƙwace yayin da Gwamnan Kano Ganduje ya hau babur ɗin KAROTA da babbar riga
A baya Legit.ng ta kawo cewa ministan harkokin ‘yan sanda, Maigari Dingyadi, ya umarci rundunar 'yan sanda da ta kawar da masu tayar da hankali a yankin kudu maso gabas da sauran wurare a Najeriya.
Dingyadi a ranar Litinin, 19 ga Afrilu, ya bayyana cewa ya ba da umarnin gudanar da binciken kwakwaf a kan masu laifin da ke kai hare-hare kan 'yan sanda.
Ya yaba wa shiyya ta 13, hedkwatar ta rundunar ‘yan sanda ta jihar Anambara kan dakile wani hari a daren Litinin wanda ya kai ga gano bindigar GPMG da ‘yan bangan suka yi amfani da ita.
Asali: Legit.ng