Kar ku ragawa kowa: FG ta umurci ƴan sanda su hukunta masu tada zaune tsaye a Kudu

Kar ku ragawa kowa: FG ta umurci ƴan sanda su hukunta masu tada zaune tsaye a Kudu

- Ministan harkokin ‘yan sanda, Maigari Dingyadi, ya mayar da martani game da hare-haren da ake kaiwa kan‘ yan sanda a kasar

- Dingyadi ya bayyana sabbin matakan da aka dauka na dakatar da kai hare-hare

- Jami’in na gwamnatin ya nuna kwarin gwiwa a kan karfin ‘yan sanda na cafke maharan da ke da alhakin aikata laifukan

Ministan harkokin ‘yan sanda, Maigari Dingyadi, ya umarci rundunar 'yan sanda da ta kawar da masu tayar da hankali a yankin kudu maso gabas da sauran wurare a Najeriya.

Dingyadi a ranar Litinin, 19 ga Afrilu, ya bayyana cewa ya ba da umarnin gudanar da binciken kwakwaf a kan masu laifin da ke kai hare-hare kan 'yan sanda.

KU KARANTA KUMA: Mako biyu da yin aurenta amarya ta fara korafi, ta ce mijinta yana aikenta barkatai

Kar ku ragawa kowa: FG ta umurci ƴan sanda su hukunta masu tada zaune tsaye a Kudu
Kar ku ragawa kowa: FG ta umurci ƴan sanda su hukunta masu tada zaune tsaye a Kudu Hoto: @MinofPoliceNG
Asali: Twitter

Ya yaba wa shiyya ta 13, hedkwatar ta rundunar ‘yan sanda ta jihar Anambara kan dakile wani hari a daren Litinin wanda ya kai ga gano bindigar GPMG da ‘yan bangan suka yi amfani da ita.

Dingyadi ya ce:

"Na yaba wa dakile harin daren da aka kai a shiyya ta 13, hedkwatar shiyyar Jihar Anambra, wanda ya kai ga dawo da bindigar GMP daya da ’yan daba suka yi amfani da ita. Na umarci jami'an leken asiri da ke jagorantar aiki, da su kawar da masu tayar da hankali a Kudu maso Gabas da sauran wurare a Najeriya.''

KU KARANTA KUMA: Tsarin rayuwarta ba ta Musulunci bace da arewa, Matashi ya soki magoya bayan Sadau

A baya Legit.ng ta kawo cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da kona wani ofishin ‘yan sanda a Uzoakoli, karamar hukumar Bende da ke jihar Abia.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Litinin, 19 ga watan Afrilu, jaridar The Nation ta ruwaito.

Yayinda ba a samu cikakken bayani kan harin ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton, an tattaro cewa ‘yan bindigar sun sha karfin‘ yan sanda da ke bakin aiki sannan suka saki masu laifin da ke tsare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel