Rikita rikita: Wasa ya ƙwace yayin da Gwamnan Kano Ganduje ya hau babur ɗin KAROTA da babbar riga
- Gwamna Ganduje ya kaddamar da mashinan da hukumar KAROTA ta saya don kula da zirga-zirga
- Gwamnan ya nuna kwarewarsa a harkar tuki yayin bikin kaddamarwar a ranar Lahadi, 19 ga Afrilu
- Ganduje ya bayyana cewa mashinan zasu kawo saukin kula da zirga-zirgar ababen hawa a jihar
Bayyanar Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano a kan babur sanye cikin 'babbar riga' ya haddasa cece-kuce a shafukan sada zumunta.
Legit.ng ta rahoto cewa gwamnan ya tunawa yan Najeriya da zamanin tsohon gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti.
KU KARANTA KUMA: Mako biyu da yin aurenta amarya ta fara korafi, ta ce mijinta yana aikenta barkatai
Fayose, a lokacin da yake mulki, an san shi da wasannin kwaikwayo daban daban wanda ke haifar da martani a shafukan sada zumunta.
Sai dai hawan babur din Gwamna Ganduje yana da wata manufa ta daban, ba kamar ta Fayose ba.
Ya hau kan daya daga cikin baburan ne lokacin da yake kaddamar da mashinan da hukumar KAROTA ta sayo don kula da zirga-zirga.
Yayin kaddamar da su a ranar Lahadi, 18 ga Afrilu, Ganduje ya ce za a yi amfani da su ne don tabbatar da cewa masu amfani da tituna sun bi ka’idojin zirga-zirga.
KU KARANTA KUMA: Kar ku ragawa kowa: FG ta umurci ƴan sanda su hukunta masu tada zaune tsaye a Kudu
Ya ce baburan za su bai wa ma’aikatan KAROTA damar motsawa cikin sauri don lura da zirga-zirga, gano masu karya doka da kuma zagaye cikin gari don kamo wadanda ke shigo da haramtattun kayayyaki zuwa jihar.
A wani labarin, yan sanda a jihar Kano sun ceto wata yarinya mai shekaru 15, Aisha Jibrin, da iyayenta suka kulle ta a daki tsawon shekaru 10 a Darerewa Quaters a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talat ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.
Asali: Legit.ng