Wata kungiyar Kiristoci ta yi Allah wadai da kagen da aka yiwa Dr Pantami

Wata kungiyar Kiristoci ta yi Allah wadai da kagen da aka yiwa Dr Pantami

- Wata kungiyar addini ta mabiya addinin kirista ta bayyana goyon bayan ta ga Dr Isa Ali Ibrahim Pantami

- Kungiyar ta bayyana cewa ana bata Ministan ne saboda sauye-sauyen da yake yi a bangaren kamfanonin sadarwa na Najeriya

- Pantami, ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani da ke cikin rudani, an zargeshi da hannu dumu-dumu a ta'addanci

Kwamitin hadin gwiwa kan kungiyoyin fararen hula da lamuran addini na Najeriya, ya yi Allah wadai da zargin alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda da aka yi wa ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ali Ibrahim Pantami.

Shugaban kwamitin, Bishop John Okafor, ya bayyana matsayarsu a cikin wata sanarwa da jaridar Vanguard ta ruwaito kuma Legit.ng ta gani a ranar Litinin, 19 ga Afrilu.

Wani bangaren, sanarwar na cewa: “Kwamitin bayan bincike ya gano cewa zarge-zargen da ake yi a kansa an yi su ne da nufin bata shi a matsayinsa na minista da kuma taba mutuncin kasar.

KU KARANTA: Duk da kasancewarsa a kurkuku, Zakzaky ya yi rabon abincin Ramadana ga mabukata

Wata kungiyar Kiristoci ta yi Allah wadai da kagen da aka yiwa Dr Pantami
Wata kungiyar Kiristoci ta yi Allah wadai da kagen da aka yiwa Dr Pantami Hoto: TVC News Nigeria
Asali: Facebook

“Hakanan ta gano cewa Dr Pantami ta kowace fuska bashi da wata alaka ta sirri da kowane mai tsattsauran ra'ayi, a matsayinsa na Shehi da jami’in gwamnati.

"Binciken majalisar ya kuma gano cewa zarge-zargen sun kasance, zanga-zanga ce kawai ta masu ruwa da tsaki, wadanda sabon sauyi da aka samu a bangaren sadarwa ya shafa, karkashin kulawar Pantami."

A cewar Bishop Okafor, Pantami Shehin addinin Islama ne, kamar yadda bishop-bishop da fastoci suke a cikin addinin kirista,.

Ya kara da cewa ministan yana wa’azi ne kamar yadda aka koyar a cikin Alkur’ani mai girma, kamar yadda masu wa’azin kirista ke yi, a cewar Littafi Mai Tsarki.

Bishop Okafor ya kuma bukaci kafafen yada labarai da su kasance masu adalci a cikin rahotanninsu da rahotanni game da masu yi wa gwamnati hidima.

KU KARANTA: Buhari ya nuna matukar damuwa kan yawaitar hatsarin tankuna a Najeriya

A wani labarin, Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Dr Isa Ali Pantami ya bukaci masoyansa da ka da su tayar da hankali game da kage da wata jarida ta yi masa na alaka da ta'addanci.

A martanin da ya yi kan zargin, ya ce ka da wani daga cikin magoya bayansa su zagi wani ko su daki wani a madadinsa.

A wani bidiyo da Legit.ng Hausa ta gano, ministan, kuma shahararren malamin addinin Islama yana cewa;

Asali: Legit.ng

Online view pixel