Buhari ya nuna matukar damuwa kan yawaitar hatsarin tankuna a Najeriya

Buhari ya nuna matukar damuwa kan yawaitar hatsarin tankuna a Najeriya

- Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna matukar damuwa kan yawaitar hatsarin manyan motoci

- Shugaban ya jajantawa al'umma da gwamnatin jihar Benue bisa hatsarin tankar mai da ya faru jiya Lahadi

- Ya kuma yi kira ga hukumomin da abin ya sahafa da su gaggauta daukar mataki nan ba da dadewa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwa kan yawaitar fashewar tankunan mai, yana mai tuhumar hukumomin da abin ya shafa da su dauki matakan gaggawa don magance lamarin, The Nation ta ruwaito.

Martanin shugaban kasar ya biyo bayan fashewar tankar da ta faru a garin Oshigbudu, yankin karamar hukumar Agatu na jihar Benue a ranar Lahadin da ta gabata, wanda ya yi sanadin mutuwar kimanin mutane 12.

A wata sanarwa daga babban hadiminsa na musamman kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, Buhari ya umarci hukumomin kula da zirga-zirgar ababen hawa da kuma Ma’aikatar Sufuri, da su nemi hanyar magance lamarin cikin gaggawa.

KU KARANTA: Azumin watan Ramadana ne ya sa 'yan bindiga suka rage kai hari, Tsohon Daraktan DSS

Buhari ya nuna matukar damuwa kan yawaitar hatsarin tankuna a Najeriya
Buhari ya nuna matukar damuwa kan yawaitar hatsarin tankuna a Najeriya Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Yayin da yake jajantawa dangin wadanda abin ya shafa, Shugaban ya ce: “Na damu da yawaitar wadannan fashewar tankuna a kan hanyoyin jama'a ko wuraren zama.

"Yakamata hukumomin kula da zirga-zirgar ababen hawa da ma'aikatun sufuri su magance wannan cikin gaggawa.”

Sanarwar ta kara yin ta’aziyya ga gwamnati da mutanen jihar Benue kan wannan lamarin, lura da cewa bai kamata a taba lamuran lafiyar jama’a ba saboda wani dalili.

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa gwamnati da mutanen jihar Benue kan fashewar tankar da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama a karamar hukumar Agatu da ke jihar.

“Ganin cewa bai kamata a gurbata lafiyar jama’a a kowane irin yanayi ba, Shugaban kasa ya yi kira da a bi ka’idoji da hanyoyin kiyaye lafiya sosai; kuma ya kamata a aiwatar da wadannan ka'idoji ba tare da tsoro ko fargaba ba," in ji sanarwar.

KU KARANTA: ‘Kada ku ji tsoron harbin bindiga’, Ministan tsaro ga dakarun sojojin Najeriya

A wani labarin, Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya ce akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa wasu jami’an gwamnatin Najeriya na hada baki da masu satar mutane don aikata mummunan aikinsu, Arise Tv ta ruwaito.

Mista Ortom ya ce 'yan siyasar da ke da wata manufa sun shigo da sojojin haya na kasashen waje don taimaka musu su ci zaben 2019. Ya lura cewa watsi da wadannan sojojin haya shi ya haifar da tabarbarewar yanayin tsaro a kasar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis lokacin da yake gabatar da lacca a Makon 'Yan Jaridu na 2021 mai taken: "Rashin tsaro a Najeriya: Maido da Zaman Lafiya, Hadin kai da Ci gaba" kuma kungiyar Hadin kan 'Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) ta shirya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.