Duk da kasancewarsa a kurkuku, Zakzaky ya yi rabon abincin Ramadana ga mabukata

Duk da kasancewarsa a kurkuku, Zakzaky ya yi rabon abincin Ramadana ga mabukata

- Duk da kasancewarsa a garkame, shugaban kungiyar Shi'a Zakzaky ya raba kayan abinci a Ramadana

- Dansa ne ya jagoranci rabon kayayyakin abincin a wasu sassan kasar ciki har da mahaifarsa Zariya

- Dan sa ya kuma bayyana cewa, wannan aiki ne da baban nasa ke yi na tsawon shekaru kuma ba zai daina ba

Shugaban Mabiya Shi’a na Kungiyar Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (IMN), Sheikh Ibraheem Zakzaky ya raba kayan abinci na miliyoyin Nairori ga mabukata albarkacin watan Azumin Ramadan, Aminiya ta ruwaito.

Dan sa Muhammad Ibraheem Zakzaky ne ya jagoranci shirin rabon kayan abincin da suka hada da buhunan Shinkafa da Sukari da Masara da Gero a madadin mahaifin nasa.

Awata takarda da ya sanya wa hannu, Muhammad Ibraheem Zakzaky ya ce mahaifin nasa ya bayar da umarnin rabon kayan Azumin ne ga mabukata.

KU KARANTA: ‘Kada ku ji tsoron harbin bindiga’, Ministan tsaro ga dakarun sojojin Najeriya

Duk da kasancewarsa a kurkuku, Zakzaky ya yi rabon abincin Ramadana ga mabukata
Duk da kasancewarsa a kurkuku, Zakzaky ya yi rabon abincin Ramadana ga mabukata Hoto: iqna.ir
Asali: UGC

Ya ce, “Mahaifina wanda yanzu haka yake tsare a gudan kurkuku, shine ya bayar da umarnin raba kayan abincin don a tallafawa mabukata a Najeriya a watan Azumin Ramadana mai Albarka.

“An kammala rabon kayan a Zariya dake jihar Kaduna da wasu Kananan Hukumomin dake fadin jihar kuma wannan wani aiki ne da mahaifin nawa ya kwashe kusan shekaru 20 yana yinsa.

“Zai ci gaba da yin haka ko da bayan gwamnatin Buhari ta shude wadda ta kashe dumbin mabiyansa da suka hada ’ya’yansa uku da aka kashe,” inji shi.

Muhammad ya kara da cewa, Malamin na taya daukacin al’ummar Musulmin duniya murnar zagayowar watan Ramadana tare da tabbatar musu da cewa suna cikin addu’o’insa a wannan wata na Azumi.

Bugu da kari, an rarraba kayan abincin a matsugunan ’yan gudun hijira dake jihohin Katsina da Zamfara.

Sauran Jihohin da suka amfana da rabon sun hada da Sakkwato da Kebbi da Kano da Filato da Nasarawa da kuma jihar Bauchi.

KU KARANTA: Buhari ya nuna matukar damuwa kan yawaitar hatsarin tankuna a Najeriya

A wani labarin, Wani tsohon Daraktan DSS, Mista Mike Ejiofor a ranar Litinin ya ce ragin hare-hare da aka samu na ’yan bindiga a duk fadin kasar na iya kasancewa sanadiyyar azumin Ramadana da ake gudanarwa a yanzu a fadin kasar.

Ramadana shi ne wata na tara a kalandar Musulunci, wanda Musulmai a duk duniya suke azumta, yin addu’o'i, komawa ga Allah, da kuma nuna soyayya ga jama’a, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Sarkin Musulmi a makon da ya gabata ya yi ishara ga fara azumin Ramadana, bayan ganin wata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.