Kar ku zagi kowa a madadi na, Dr. Pantami yayi raddi kan zarginsa da ta'addanci

Kar ku zagi kowa a madadi na, Dr. Pantami yayi raddi kan zarginsa da ta'addanci

- Minista Dr Pantami ya mai da martani kan kage da wata jarida ta yi masa ta alaka da ta'addanci

- Ya gargadi masoyansa da cewa, kada su mai da martani ko hantarar wani a kan abinda ya faru

- A cewar ministan, duk wanda ya zo da wata magana da ba gaskiya ba kada a dauke ta kuma yi masa nasiha

Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Dr Isa Ali Pantami ya bukaci masoyansa da ka da su tayar da hankali game da kage da wata jarida ta yi masa na alaka da ta'addanci.

A martanin da ya yi kan zargin, ya ce ka da wani daga cikin magoya bayansa su zagi wani ko su daki wani a madadinsa.

KU KARANTA: Zulum ya raba abinci da tsabar kudi ga iyalai 9,400 cikin watan Ramadana a Mafa

Kar ku zagi kowa a madadi na, Dr. Pantami yayi raddi kan zarginsa da ta'addanci
Kar ku zagi kowa a madadi na, Dr. Pantami yayi raddi kan zarginsa da ta'addanci Hoto: theguardian.ng
Asali: UGC

A wani bidiyo da Legit.ng Hausa ta gano, ministan, kuma shahararren malamin addinin Islama yana cewa;

"Duk wanda yake tare ban yarda ya zagi wani ba, ban yarda ya yi wa wani kazafi ba, ban yarda ya aibata wani ba, ban yarda ya daki wani ba, ban yarda ya yi komai ba.

"Idan mutum ya yi maganar da ka ga bai dace ba; ka yi masa nasiha. Idan ya zo da labarin da bai dace ba ko gaba da gaba ne ko a rubuce ne kace masa ba haka bane ka gyara. Idan ya dauka fani'ima idan bai dauka ba shi da Allah.

"Ba anan zamu tabbata ba, akwai wata rayuwa bayan wannan ta duniya."

A makon da ya gabata ne wata jarida ta wallafa cewa, an ga sunan Dr Pantami cikin jerin wadanda ke da hannu a ta'addancin Al-Qa'eeda, lamarin da ya jawo cece-kuce.

KU KARANTA: Ramadana: Kwamishina ya bada tallafin N23m ga mutane sama da 3,000 a Katsina

A wani labarin, A safiyar yau ne NewsWireNGR ta buga cewa, gwamnatin kasar Amurka ta sanya sunan Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Dr Isa Ali Ibrahim Pantami cikin jerin masu hannu cikin tashin tashina na Boko Haram.

Bayan da jaridar ta lashe amanta biyo bayan cece-kuce, ta bayyana janye labarin da ta fitar, amma Dr Isa Ali Pantami ya mai da martani kan rubutun da jaridar ta wallafa.

Ya rubuta a shafinsa na Tuwita cewa: "@NewsWireNGR Janye rubutunku ta hanyar binciken ka mai zaman kansa, na lura dashi. Ko da yake, aikin jarida na bincike yana bukatar bincike kafin a buga shi, ba bayan an buga ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel