Rikicin kabilanci ya sake ballewa a wani yankin jihar Gombe, an kona gidaje 50
- 'Yan bindiga sun kai hari wani yankin jihar Gombe, in da aka kone gidaje akalla 50 sakamakon fadan kabilanci
- Rikici ne na kabilanci ya jawo sabbin hare-haren a yankin, in da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 19
- Kwamishinan 'yan sanda a jihar ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce jami'ansa sun shawo kan lamarin
A wani harin 'yan bindiga, akalla gidaje 50 ne suka kone tare kayan gona a wani sabon rikicin kabilanci a garin Nyuwar, na Jessu da ke jihar Gombe, The Punch ta ruwaito.
Ku tuna cewa an kashe mutane 19 tare da daruruwan gidaje da ba a san ko su waye suka lalata ba a rikicin Waja/Lunguda.
Wani shaidar gani da ido, Ily Maisanda, ya ce tuni mazauna garin suka tafi Yolde don tsare kansu, in da ‘yan bindigan suka yi amfani da wannan dama wajen kai sabon hari a Nyuwar ranar Lahadi.
KU KARANTA: Kar ku zagi kowa a madadi na, Dr. Pantami yayi raddi kan zarginsa da ta'addanci
Maisanda ya ce, “Mazauna garin na iya ganin wutar daga Yolde. Wasu daga cikinsu (maharan) an kama su a cikin Cham bayan sun kwashe hatsi daga gidajen da ba kowa.
“A halin yanzu, babu wani taimako da ke zuwa daga gwamnati; magana kawai suke yi, rikici ne mai zafi.”
Wani mazaunin, Musa James ya ce, “Dare ne da ba hutu saboda wasu sassan Nyuwar-Sakku Luko, da wasu gidaje na Lunguda sun sake konewa.
Hakanan, wani Dennis Kujir ya kara da cewa 'yan bindigar sun afkawa kauyukan a ranar Asabar da safiyar Lahadi.
Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Ishola Babaita, ya tabbatar da harin, ya kara da cewa mutanen sa sun dakatar da karin barna.
KU KARANTA: Jihar Adamawa ta dakatar da albashin malamai sama da 2,000 da zargin na bogi ne
A wani labarin, Rundunar tsaro ta hadin gwiwa a karamar hukumar Shiroro da ke jihar Neja ta kashe 'yan bindiga shida a yayin wani samame na dakile harin da 'yan ta'addan suka kai a yankin Garkogo, The Nation ta ruwaito.
An ce 'yan bindigar sun kai hari a wasu kauyukan da ke kusa da Garkogo amma rundunar hadin gwiwar ta fatattake su.
Bayanai sun ce rundunar ta dauki matakin ne bayan wani labari da ta samu kan harin da aka kai kauyukan a safiyar ranar Asabar inda suka yi kwanto da ‘yan bindigan.
Asali: Legit.ng