Jihar Adamawa ta dakatar da albashin malamai sama da 2,000 da zargin na bogi ne

Jihar Adamawa ta dakatar da albashin malamai sama da 2,000 da zargin na bogi ne

- Gwamnatin jihar Adamawa ta dakatar da malaman da take zargin na bogi ne sama da 2,000 a jihar

- Gwamnatin ta gudanar da bincike ne a ma'aikatar ilimi na jihar in da ta gano lamarin cikin sauki

- Hakazalika ta ce ba ta ayyanasu a matsayin ma'aikatan bogi ba, amma ta dakatar da albashinsu

Gwamnatin Jihar Adamawa ta ce ta dakatar da albashin ma’aikata sama da dubu biyu wadanda ba su shiga tsarin tantance albashi da kuma daukar bayana da Gwamna Ahmadu Fintiri ya bayar ba.

Kwamishinan Kudi na jihar, Ishaya Dabari da kuma Akanta Janar na jihar, Kefas Tagwi, a ranar Juma’a sun musanta cewa rashin biyan ma’aikatan na da nasaba da yarjejeniyar da aka sanya a asusun da gwamnatin jihar ke sarrafawa da wasu bankunan kasuwanci.

Dabari, ya ce gwamnatin jihar tana jin kunyar bayyana ma’aikatan da ba su sami albashin su a watan Maris ba cewa ma’aikatan bogi ne saboda girman lamarin a wurin gwamnan, The Punch ta ruwaito.

KU KARANTA: Abubawan da ke jawo hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya

Jihar Adamawa ta dakatar da albashin malamai sama da 2,000 da zargin na bogi ne
Jihar Adamawa ta dakatar da albashin malamai sama da 2,000 da zargin na bogi ne Hoto: akelicious.net
Asali: UGC

Kwamishinan ya ce, “Gwamna Fintiri, da ke karfafa nuna gaskiya da rikon amana a cikin sha’anin mulki, ya ba da umarnin daukar bayanai ta na’urar tantance bayanai da kuma bincikar biyan ma’aikata ga dukkan ma’aikatan gwamnati a dukkan ma’aikatu, sassa da hukumomi.

“Amma tunda zai gudana mataki-mataki ne, aikin ya fara ne da kwamitin gudanarwa na makarantun gaba da firamare na malamai a makarantun sakandare a jihar.

"Da farko, muna da malamai sama da 12,000, wanda shine adadin da ke cikin tsarin biyan mu.

“Amma bayan tantancewar, mun iya tabbatar da sama da malamai 9,000, wanda ya bayyana cewa sama da malamai 2,000 ba asan in da suke ba.

"Abin da muka yi a cikin hikimarmu ba mu ayyana ma'aikatan a matsayin ma'aikatan bogi ba. Amma dai, an dakatar da albashin ma’aikatan da abin ya shafa wadanda ba su zo don tantancewa ba da kuma ba da bayanansu ba.”

KU KARANTA: 'Yan matan Chibok da aka sake da yawansu suna can suna karatu a jami'a, Tallen

A wani labarin, Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Aisha Bello Muhammad Matawalle ta tabbatar da nadin mataimaka na musamman ga gwamna Bello Matawalle ga mambobi 20 na kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) a jihar.

Mai magana da yawun uwargidan shugaban kasar, Zainab Abdullahi, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata, ChannelsTv ta ruwaito.

Da yake jawabi a madadin wadanda aka nadan, Shugaban kungiyar na jihar, Alhaji Tukur Abubakar ya yaba wa Uwargidan Gwamnan kan kokarinta na samar da canji mai ma’ana ga Fulani da sauran jama’ar gari, in ji sanarwar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel