Nasara daga Allah: 'Yan sanda sun sheke 'yan bindiga 6 a jihar Neja
- Rundunar 'yan sanda a jihar Neja ta hallaka 'yan bindiga 6 a wani samame kan 'yan bindiga
- An bayyana mutuwar hudu daga ciki nan take, biyu kuwa an tsince su a daji matattu murus
- Rundunar 'yan sandan jihar har zuwa yanzu basu fidda wata sanarwa game da lamarin ba
Rundunar tsaro ta hadin gwiwa a karamar hukumar Shiroro da ke jihar Neja ta kashe 'yan bindiga shida a yayin wani samame na dakile harin da 'yan ta'addan suka kai a yankin Garkogo, The Nation ta ruwaito.
An ce 'yan bindigar sun kai hari a wasu kauyukan da ke kusa da Garkogo amma rundunar hadin gwiwar ta fatattake su.
Bayanai sun ce rundunar ta dauki matakin ne bayan wani labari da ta samu kan harin da aka kai kauyukan a safiyar ranar Asabar inda suka yi kwanto da ‘yan bindigan.
KU KARANTA: Ramadana: Kwamishina ya bada tallafin N23m ga mutane sama da 3,000 a Katsina
An ce wasu 'yan bindigan da dama sun tsere da munanan raunuka na harsashi kamar yadda suka gudu daga kauyukan a kan babura.
Wannan nasarar ta rundunar tsaro ta hadin guiwa na zuwa ne makonni uku bayan da wasu 'yan bindiga suka kai hari sansanin rundunar tare da kashe sojoji biyar da dan sanda daya a Allawa.
An samu labarin cewa an kashe hudu daga cikin 'yan bindigan a nan take yayin da aka ga gawarwakin mutum biyu a gona yayin da aka ce sun mutu ne sakamakon raunin harbin bindiga.
Har yanzu rundunar ‘yan sandan Neja ba ta fitar da wata sanarwa game da lamarin ba.
Kiraye-kiraye da sako da aka aike wa jami’in hulda da jama’a na ’yan sandan Neja, DSP Wasiu Abiodun ba a amsa su ba a lokacin hada wannan rahoton.
KU KARANTA: Zulum ya raba abinci da tsabar kudi ga iyalai 9,400 cikin watan Ramadana a Mafa
A wani labarin, A ranar Asabar ne wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kashe dan sandan dake tare da Shoban Tikari, shugaban karamar hukumar Takum na jihar Taraba, yayin da suka bude wuta kan motar shugaban a kauyen Dogo-Gawa da ke yankin karamar hukumar Takum.
Dan sandan da ya mutu yana daga cikin rundunar 'yan sanda ta mobal ta 67, da ke yankin, Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng