Ramadana: Kwamishina ya bada tallafin N23m ga mutane sama da 3,000 a Katsina

Ramadana: Kwamishina ya bada tallafin N23m ga mutane sama da 3,000 a Katsina

- Wani kwamishina a jihar Zamfara ya gwangwaje al'ummar wasu kananan hukumomin jihar

- An ruwaito cewa, kwamishinan ya rabawa mutane akalla 3,104 makudan kudade kusan N23m

- A wurin rabon, ya roki jama'a da su sanya gwamnatin jihar a addu'o'i cikin Ramadana don samun zaman lafiya

Akalla mutane 3104 marasa karfi a kananan hukumomi hudu na jihar Katsina sun amfana da gudummawar kudi naira miliyan 23 da Kwamishinan Muhalli, Alhaji Hamza Sule Faskari ya bayar.

An bayar da tallafin ne ga mutanen don rage musu wahalar fafutukar rashin kudi a lokacin watan Ramadan., Daily Trust ta ruwaito.

Da yake jawabi lokacin raba kudaden a karshen mako, kwamishinan ya bayyana cewa an zabo wadanda suka amfana da rabon a hankali daga Faskari, Sabuwa, Kankara, Dandume da wasu sassan kananan hukumomin Funtua.

KU KARANTA: Abubawan da ke jawo hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya

Ramadan: Kwamishina ya bada tallafin N23m ga mutane sama da 3,000 a Katsina
Ramadan: Kwamishina ya bada tallafin N23m ga mutane sama da 3,000 a Katsina Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

"Mun zo ne don yaba wa kokarin jagoranmu, Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, na rage wahalhalun da mutane ke sha musamman a lokacin watan Ramadan mai alfarma," in ji shi.

“Gwamna Masari ya kasance yana nuna damuwa kan rashin tsaro a yankinmu. Gwamnatinsa na yin iya kokarinta don ganin an dawo da al’amuran yau da kullun a yankin,” ya kara da cewa.

Daga nan sai Faskari ya yi kira ga mazauna yankin da su yi amfani da wannan wata na musamman na Ramadan don yin addu’a ga shugabanni, hukumomin tsaro da kuma zaman lafiya ya dawo yankin.

Ya kuma godewa matar gwamnan jihar, Hajiya Hadiza Aminu Bello Masari, wacce da kanta ta halarci bikin.

A nasa jawabin, mataimakin shugaban jam'iyyar APC na shiyyar Funtua, Alhaji Bala Abu Musawa, ya yaba wa kwamishinan bisa wannan karimcin.

“Hamza ba shi kadai aka nada daga shiyyar mu ba, amma ya nuna yana da kwazo a cikin daidaiku. Wannan shi ne karo na biyar da yake bayar da tallafi ga mazabarsa,” in ji shi.

Shima da yake jawabi, mai baiwa gwamnan jihar shawara na musamman kan harkokin zamantakewar al'umma, Alhaji Abdulqadir Mammam Nasir, ya yaba wa kwamishinan kan shiga tsakani wajen tallafawa marasa karfi a jihar.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun bindige dan sanda dogarin shugaban karamar hukuma a jihar Taraba

A wani labarin, A ranar Asabar da ta gabata ne gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya rabawa iyalai sama da 9,400 kayayyakin abinci da tsabar kudi a yankin Mafa na jihar.

Kowane daga cikin maza 3,500 da suka ci gajiyar rabon sun sami buhun shinkafa, buhun garin masara na da kuma kudi, yayin da kowacce daga cikin mata 5,900 da suka ci gajiyar rabon suka sami zane, fakiti 2 na sukari da kudi.

Hakazalika ya duba wasu ayyukan da ke gudana, wadanda suka hada da shirin noman rani, cibiyar koyar da sana’o’i, rukunin shagunan kasuwanci, da kuma tashar mota tare da rumfunan kasuwa 150.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel