Zulum ya raba abinci da tsabar kudi ga iyalai 9,400 cikin watan Ramadana a Mafa

Zulum ya raba abinci da tsabar kudi ga iyalai 9,400 cikin watan Ramadana a Mafa

- Gwamnan jihar Borno ya kai ziyara yankin Mafa, in da ya raba abinci da tsabar kudade ga al'ummar

- Akalla mutane 9,400 ne suka ci gajiyar rabon da ya yi a jiya Asabar yayin ziyarar da ya kai

- Ya kuma bukaci al'ummar yankin da su dage da addu'a a watan Ramadana don dawo da zaman lafiya

A ranar Asabar da ta gabata ne gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya rabawa iyalai sama da 9,400 kayayyakin abinci da tsabar kudi a yankin Mafa na jihar.

Kowane daga cikin maza 3,500 da suka ci gajiyar rabon sun sami buhun shinkafa, buhun garin masara na da kuma kudi, yayin da kowacce daga cikin mata 5,900 da suka ci gajiyar rabon suka sami zane, fakiti 2 na sukari da kudi.

Hakazalika ya duba wasu ayyukan da ke gudana, wadanda suka hada da shirin noman rani, cibiyar koyar da sana’o’i, rukunin shagunan kasuwanci, da kuma tashar mota tare da rumfunan kasuwa 150.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Najeriya ce ta 1 a shigo da kayayyaki daga kasashen waje, WTO

Zulum ya raba abinci da tsabar kudi ga iyalai 9,400 da suka rasa muhallansu a Mafa
Zulum ya raba abinci da tsabar kudi ga iyalai 9,400 da suka rasa muhallansu a Mafa Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

Gwamna Zulum ya yi jawabi ga mazauna yankin, inda ya bukace su da su yi amfani da wannan wata mai alfarma na Ramadan tare da yin addu’ar dawowar zaman lafiya a Borno da ma kasa baki daya.

Zulum ya raba abinci da tsabar kudi ga iyalai 9,400 da suka rasa muhallansu a Mafa
Zulum ya raba abinci da tsabar kudi ga iyalai 9,400 da suka rasa muhallansu a Mafa Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

Legit.ng Hausa ta gano inda gwamnan ke cewa:

"Ina mai kira a gare ku baki daya da ku kara dagewa da addu'oinku a wannan wata na Ramadana mai alfarma, ya kamata dukkanmu mu dukufa cikin addu'o'in neman zaman lafiya ya dawowa jiharmu da kasarmu."

Gwamnan ya kuma bayyana godiyarsa ga Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabashi kan karin kokarin da Gwamnatin Jiha take yi.

Zulum ya raba abinci da tsabar kudi ga iyalai 9,400 da suka rasa muhallansu a Mafa
Zulum ya raba abinci da tsabar kudi ga iyalai 9,400 da suka rasa muhallansu a Mafa Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

KU KARANTA: Abubawan da ke jawo hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya

A wani labarin, Gwamnatin Jihar Adamawa ta ce ta dakatar da albashin ma’aikata sama da dubu biyu wadanda ba su shiga tsarin tantance albashi da kuma daukar bayana da Gwamna Ahmadu Fintiri ya bayar ba.

Kwamishinan Kudi na jihar, Ishaya Dabari da kuma Akanta Janar na jihar, Kefas Tagwi, a ranar Juma’a sun musanta cewa rashin biyan ma’aikatan na da nasaba da yarjejeniyar da aka sanya a asusun da gwamnatin jihar ke sarrafawa da wasu bankunan kasuwanci.

Dabari, ya ce gwamnatin jihar tana jin kunyar bayyana ma’aikatan da ba su sami albashin su a watan Maris ba cewa ma’aikatan bogi ne saboda girman lamarin a wurin gwamnan, The Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.