'Yan bindiga sun bindige dan sanda dogarin shugaban karamar hukuma a jihar Taraba

'Yan bindiga sun bindige dan sanda dogarin shugaban karamar hukuma a jihar Taraba

- Wani dan sanda da ke tare shugaban wata karamar hukumar Takum a Taraba ya riga mu gidan gaskiya

- 'Yan bindiga sun bude wuta kan motar shugaban karamar hukumar Takum inda suka hallaka dan sandan

- Shugaban karamar hukumar ya ki bayyana sunan dan sandan, ya kuma yi kira ga gwamnati ta kara jami'an tsaro a yankin

A ranar Asabar ne wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kashe dan sandan dake tare da Shoban Tikari, shugaban karamar hukumar Takum na jihar Taraba, yayin da suka bude wuta kan motar shugaban a kauyen Dogo-Gawa da ke yankin karamar hukumar Takum.

Dan sandan da ya mutu yana daga cikin rundunar 'yan sanda ta mobal ta 67, da ke yankin, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Ahmed Lawan: Shugabanni na bukatar addu'o'inku talakawa don shawo kan matsaloli

'Yan bindiga sun bindige dan sanda dogarin shugaban karamar hukuma a jihar Taraba
'Yan bindiga sun bindige dan sanda dogarin shugaban karamar hukuma a jihar Taraba Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Tikari, wanda ya tabbatar da faruwar harin, ya ce 'yan bindigan da ke tafe da yawa, sun kai hari a kan ayarin motocinsa yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Takum, inda suka kashe dan sandan.

Shugaban wanda ya ki bayyana sunan mamacin, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tura karin jami’an tsaro yankin.

Kananan hukumomin Takum da Wukari, a kudancin Taraba a cikin 'yan kwanakin nan sun sha fama da yawan hare-haren 'yan bindiga da ke haifar da mutuwar fararen hula da jami'an tsaro.

KU KARANTA: Zulum ya raba abinci da tsabar kudi ga iyalai 9,400 cikin watan Ramadana a Mafa

A wani labarin, Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya ce akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa wasu jami’an gwamnatin Najeriya na hada baki da masu satar mutane don aikata mummunan aikinsu, Arise Tv ta ruwaito.

Mista Ortom ya ce 'yan siyasar da ke da wata manufa sun shigo da sojojin haya na kasashen waje don taimaka musu su ci zaben 2019. Ya lura cewa watsi da wadannan sojojin haya shi ya haifar da tabarbarewar yanayin tsaro a kasar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis lokacin da yake gabatar da lacca a Makon 'Yan Jaridu na 2021 mai taken: "Rashin tsaro a Najeriya: Maido da Zaman Lafiya, Hadin kai da Ci gaba" kuma kungiyar Hadin kan 'Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) ta shirya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel