Ahmed Lawan: Shugabanni na bukatar addu'o'inku talakawa don shawo kan matsaloli

Ahmed Lawan: Shugabanni na bukatar addu'o'inku talakawa don shawo kan matsaloli

- Shugaban majalisar dattijai ya bukaci talakawa 'yan Najeriya da su sanya shugabanni a addu'a

- Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin shugaba Buhari tana iya kokarinta wajen inganta kasar nan

- Ya bayyana haka ne a wani taron kaddamar da aikin masallacin masarautar Potiskum a jihar Yobe

Shugaban majalisar dattijai, Dakta Ahmad Lawan ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa shugabannin gwamnati addu’a a kokarinsu na tunkarar matsaloli daban-daban da kasar ke fuskanta, This Day ta ruwaito.

Lawan ya yi wannan kira ne a jiya Asabar a wajen kaddamar da asusun tallafi na Masallacin Masarautar Potiskum a garin Potiskum dake Jihar Yobe.

Shugaban majalisar dattijan da ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 20 don tallafawa aikin ya ce: “A kowane lokaci shugabanni na bukatar addu’o’i musamman daga mabiya.

KU KARANTA: Abubawan da ke jawo hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya

Ahmed Lawan: Shugabanni na bukatar addu'o'inku talakawa don shawo kan matsaloli
Ahmed Lawan: Shugabanni na bukatar addu'o'inku talakawa don shawo kan matsaloli Hoto: ripplesnigeria.com
Asali: UGC

“Shugabanninmu, musamman Shugaban kasarmu, Muhammadu Buhari, da fatan Allah Ya ba shi lafiya, Allah Ya ba shi jagorancin kasar nan ne ta dalilinku.

“Yana kokari iyakar kokarinsa a gare ku kuma mu ma da muke daga bangaren shugabancinsa, muna kokari iyakar kokarinmu don ganin cewa abubuwa sun daidaita a Najeriya.

“Don haka zan yi amfani da wannan damar in roke ku da ku ci gaba da yi wa shugabanninmu addu’a cewa Allah Madaukaki ya ci gaba da yi musu jagoranci yayin da suke fuskantar hanyoyin magance matsalolin tsaro, rashin aikin yi ga matasa da kuma ci gaba da taimaka wa mutanenmu.

“Haka nan tare da jihar mu, jihar Yobe, abin alfaharin mu. Cewa Gwamnanmu, Mai Mala Buni yana iya kokarinsa don tabbatar da ci gaban jihar. Sanin kowa ne cewa akwai ayyukan ci gaba a kowane bangare na jihar,” in ji Lawan.

Lawan ya kuma bayyana cewa Sanata Sani Musa ya bayar da gudummawar naira miliyan biyar yayin da Sanata Bello Mandiya da Sadiq Suleiman suka bayar da miliyan daya kowannensu wajen aikin ginin.

KU KARANTA: Jihar Adamawa ta dakatar da albashin malamai sama da 2,000 da zargin na bogi ne

A wani labarin, A ranar Asabar da ta gabata ne gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya rabawa iyalai sama da 9,400 kayayyakin abinci da tsabar kudi a yankin Mafa na jihar.

Kowane daga cikin maza 3,500 da suka ci gajiyar rabon sun sami buhun shinkafa, buhun garin masara na da kuma kudi, yayin da kowacce daga cikin mata 5,900 da suka ci gajiyar rabon suka sami zane, fakiti 2 na sukari da kudi.

Hakazalika ya duba wasu ayyukan da ke gudana, wadanda suka hada da shirin noman rani, cibiyar koyar da sana’o’i, rukunin shagunan kasuwanci, da kuma tashar mota tare da rumfunan kasuwa 150.

Asali: Legit.ng

Online view pixel