Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa ya kammala cibiyar wasanninsa ta miliyoyin naira a Kaduna

Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa ya kammala cibiyar wasanninsa ta miliyoyin naira a Kaduna

- Ahmed Musa shine kyaftin din Super Eagles na Najeriya

- Tsohon tauraron dan wasan na Leicester City ya kammala cibiyar wasanninsa a jihar Kaduna

- Musa zai kuma buga wa Kano Pillars wasa a zagaye na biyu na NPFL

Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa ya kammala cibiyarsa ta wasanni ta miliyoyin naira a Kaduna inda ake sa ran matasa za su samu horo kuma za su iya baje kolin baiwarsu ma.

Tsohon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Leceister City yana daya daga cikin attajiran yan wasan Najeriya idan aka yi la’akari da kadarorin sa tun lokacin da ya fara wasan kwallon kafa daga titin garin Jos.

KU KARANTA KUMA: Tafiyar ganin likita a Ingila: Daga ƙarshe FG ta magantu game da dawowar Shugaba Buhari

Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa ya kammala cibiyar wasanninsa ta miliyoyin naira a Kaduna
Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa ya kammala cibiyar wasanninsa ta miliyoyin naira a Kaduna Hoto: Alex Morton
Asali: Getty Images

Ahmed Musa ya fara wasan kwallon kafa a garin Jos kafin ya koma kungiyar JUTH FC daga inda tsohon zakaran gasar kwallon kafa ta Kano Pillars ya sanya masa hannu.

Shekara daya kawai yayi Sai Masugida wanda ya ci kwallaye 18 kafin ya koma Turai inda ya samu kudi mai tsoka ga kansa.

Musa wanda ya buga wasansa na karshe a gasar Saudiyya yana da cibiyar wasanni ta miliyoyin naira a jihar Kano.

Matashin mai shekaru 28 ya kuma dauki nauyin dalibai 100 a Kano don samun digiri a jami'a wanda hakan wani abin birgewa ne ga kyaftin din Super Eagles.

KU KARANTA KUMA: Ku je ku rarrashe shi: PDP ta tura Tambuwal, Obaseki da Saraki zuwa Cross River don ganawa da Ayade

A wani labarin, Ahmed Musa, ya kammala rattafa hannu kan kwantiragin komawa kungiyar kwallon Kano Pillars, zuwa karshen kakar 2020/2021 na NPFL.

Shugabannin kungiyar sun tabbatar da hakan a daren Litinin.

Bisa jawabin da ya fito daga ofishin shugaban kungiyar, Surajo Jambul, kuma jami'in yada labaran kungiyar, Rilwani Idris Malikawa, ya rattafa hannu, sun yanke shawaran dauko Ahmed Musa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel