Ku je ku rarrashe shi: PDP ta tura Tambuwal, Obaseki da Saraki zuwa Cross River don ganawa da Ayade

Ku je ku rarrashe shi: PDP ta tura Tambuwal, Obaseki da Saraki zuwa Cross River don ganawa da Ayade

- Rahotanni sun nuna cewa shugabancin jam'iyyar PDP sun dauki matakai don dakatar da sauya shekar da Gwamna Ayade ke shirin yi zuwa APC

- An rahoto cewa gwamnan na Cross River yana shirin sauya sheka bayan da ya rasa iko da tsarin jam'iyyar a taron jihar da aka gudanar kwanan nan

- Shugabannin kananan hukumomi da kansiloli masu biyayya ga Ayade suma sun yi barazanar bin gwamnan zuwa duk jam'iyyar da ya yanke shawarar komawa

Wani rahoto da jaridar Thisday ta fitar ya nuna cewa gwamnan jihar Cross River, Ben Ayade, na shirin sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Jaridar ta lura cewa wannan matakin da gwamnan ya dauka ya biyo bayan rasa ikon jan ragamar tsarin PDP a jihar ga mambobin jam'iyyar a majalisar dokokin kasa lokacin taron da aka gudanar kwanan nan.

KU KARANTA KUMA: Tashin hankali: An gano gawawwaki ba tare da kai ba a karkashin gada a Cross River

Ku je ku rarrashe shi: PDP ta tura Tambuwal, Obaseki da Saraki zuwa Cross River don ganawa da Ayade
Ku je ku rarrashe shi: PDP ta tura Tambuwal, Obaseki da Saraki zuwa Cross River don ganawa da Ayade Hoto: @senatorbenayade
Asali: Twitter

An tattaro cewa dukkanin shugabannin kananan hukumomi 18 da kansiloli 196 a yankin kudu maso kudu na biyayya ga gwamna Ayade kuma sun yi barazanar bin gwamnan idan ya yanke shawarar komawa wata jam'iyyar.

Don kauce wa gagarumin sauya shekar, Kwamitin PDP na kasa (NWC) ya tattara Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato da Godwin Obaseki na jihar Edo da kwamitin sulhu na jam’iyyar karkashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattijai, Dr Bukola Saraki, don shawo kan Gwamna Ayade domin ya sake tunani a kan shirinsa.

Sai dai kuma, shugabannin kananan hukumomin da kansilolin sun shaida wa NWC cewa hanyar da za a bi don hana sauya sheka ita ce a gudanar da sabbin taruka a dukkan matakai a jihar.

An ruwaito cewa shugaban karamar hukumar Calabar, Effiong Eke, ya fadawa manema labarai bayan ganawa da kwamitin NWC cewa sun bukaci a sake sabon taron majalisar jiha don tabbatar da dawowar tsarin jam’iyyar ga Gwamna Ayade.

Ya ce:

“Gwamnan shi ne shugaban jam’iyyar a jihar. Yakamata a bashi ikon jan ragamar jam'iyyar kuma ana iya yin hakan ne kawai da sabon taro.

“Muna neman a sake sabon taro. Idan ba haka ba, inda gwamna, Farfesa Ben Ayade, ya je, za mu tafi tare da shi. Shine shugaban jam’iyyar a jihar.”

KU KARANTA KUMA: Fasto Adeboye ya bayyana gaskiyar lamari game da Gwamna El-Rufai

A gefe guda, yayin da ake rade-radin cewa gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, zai bar jam’iyyar PDP, Dr. Suleiman Shuaibu Shinkafi ya yi fashin baki.

Shugaban kungiyar Concerned APC Youth ta Najeriya, Suleiman Shuaibu Shinkafi ya bayyana cewa gwamna Bello Matawalle ba zai iya barin PDP ba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Dr. Suleiman Shuaibu Shinkafi ya na cewa tilas sai gwamnan ya ajiye mukaminsa idan ya na so ya shiga jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel