Tafiyar ganin likita a Ingila: Daga ƙarshe FG ta magantu game da dawowar Shugaba Buhari

Tafiyar ganin likita a Ingila: Daga ƙarshe FG ta magantu game da dawowar Shugaba Buhari

- Ana ci gaba da yin martani game da tafiyar ganin likita da Shugaba Buhari yayi zuwa Landan, kasar Burtaniya

- Wasu ‘yan Najeriya sun caccaki shugaban kasar saboda rashin zuwa neman lafiya a cikin kasar

- Sai dai kuma, fadar shugaban kasa ta dage kan cewa Buhari na da ‘yancin zuwa neman lafiya a ko’ina

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa babu wani babban abun damuwa game da lokacin da ake sa ran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai dawo Najeriya daga tafiyarsa ta jinya a Landan, Ingila.

Shugaban Najeriyan ya tafi kasar Ingila domin duba lafiyarsa a ranar Talata, 30 ga Maris, 2021, inda fadar shugaban kasar ta ba da tabbacin cewa zai dawo Abuja a tsakiyar watan Afrilu.

KU KARANTA KUMA: Ta shiga matsala: An yi kuskuren tura mata N456m, ita kuma ta sayi gida da mota

Tafiyar ganin likita a Ingila: Daga ƙarshe FG ta magantu game da dawowar Shugaba Buhari
Tafiyar ganin likita a Ingila: Daga ƙarshe FG ta magantu game da dawowar Shugaba Buhari Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Sai dai kuma, bayan kwanaki 15 a Landan, har yanzu ba a san lokacin da shugaban zai dawo ba.

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, a ranar Laraba, 14 ga Afrilu, ya ki bayyana wani takamaiman ranar da Buhari zai dawo kasar daga Landan, jaridar This Day ta ruwaito.

A cewar jaridar This Day, lokacin da aka tambaye shi game da batun bayan taron Majalisar Zartarwa na Tarayya (FEC), Mohammed ya ce:

“Yau Laraba, wannan makon zai kare a ranar Asabar. Don haka, menene babban abun damuwa a kan wannan? "

Ministan ya bayyana cewa a halin yanzu gwamnati ta fi damuwa da matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta, jaridar The Punch ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Ku je ku rarrashe shi: PDP ta tura Tambuwal, Obaseki da Saraki zuwa Cross River don ganawa da Ayade

A wani labarin kuma, Ƙungiyar dake kare haƙƙin ƙananan yara, UNICEF, ta roƙi yan Najeriya waɗanda aka yi ma rigakafin COVID19 ta AstraZeneca a karon farko da su koma a sake yi musu ita a karo na biyu.

Ƙungiyar dake taimaka ma yara da kuma ɗalibai,UNICEF, ta ce sake yin allurar zai ƙara ma kwayoyin halittar jikin mutum ƙarfi su yaƙi cutar yadda ya kamata.

Elizabeth Onitolo, wanda ta ƙware kan harkar sadarwa domin kawo cigaba a UNICEF, ita ce ta yi wannna kiran ranar Laraba a Yola a wurin taron kwana uku akan allurar rigakafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel