Kuri'un talakawa ya kamata su tattance zabe ba kotu ba, in ji Jonathan

Kuri'un talakawa ya kamata su tattance zabe ba kotu ba, in ji Jonathan

- Tsohon shugaban kasa Goodluck jonathan ya bayyana ra'ayinsa kan ba kotu damar tantance zabe

- Ya yi kira ga samar da dokar ta za ta barranta daga bai wa kotuna bayyana sakamakon zabe

- Ya yi jawabin ne a shahinsa kan soke zaben jihar Imo da kotu ta soke na nasarar jam'iyyar PDP

Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya ba da shawarar bukatar yin dokar da za ta hana kotuna bayyana wanda ya ci zabe, gidan talabijin na Channels ta ruwaito.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Litinin a Abuja, Jonathan ya dage kan cewa yanayin da aka ba wa bangaren shari’a damar bayyana wadanda suka ci zabe saboda magudi bai kamata a kyamace shi ba, saboda ya saba wa dimokiradiyya.

KU KARANTA: Zulum da Sanatocin Borno sun ziyarci CDS da COAS kan batun Boko Haram

Kuri'un talakawa ya kamata su tattance zabe ba kotu ba, in ji Jonathan
Kuri'un talakawa ya kamata su tattance zabe ba kotu ba, in ji Jonathan Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya ce : "Na riga na yi bayani a bainar jama'a a kan hakan don cewa takardar jefa kuri'a ba bangaren shari'a ba ne zai tantance wanda zai ci zabe ko kuma ya zabi shugabannin siyasa. Kamata ya yi takardar zaben ta kasance ita kadai ce tushen zabar shugabannin siyasa."

An shigar da kararraki da dama a gaban kotu a kan lamuran da suka shafi fafatawa a tsakanin jam'iyyun.

A baya kotun koli ta soke zaben Emeka Ihedioha na jam'iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Imo .

Kotun ta kuma bayyana Hope Uzodinma na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka yi a ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2020.

Yayin da yake kokawa kan halin da 'yan siyasa ke amfani da kyauta don yaudarar masu jefa kuri'a yayin gudanar da zabe, tsohon shugaban kasar ya bukaci daukar matakan hukunta wadanda suka tsunduma cikin mummunan halin.

KU KARANTA: Mutanen gari sun kona wasu 'yan bindiga kurmus da ransu a jihar Katsina

A wani labarin, Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya gargadi ‘yan siyasa a kasar nan kan yin alkawuran karya ga talakawan Najeriya yayin neman zabe a ofisoshin gwamnati, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Ya yi wannan gargadin ne a ranar Asabar a Bori, hedikwatar karamar hukumar Khana ta jihar Ribas.

“Lokaci ya yi; lokacin da idan kuka yi wa mutane alkawari, dole ne ku cika alkawarin. Don haka, ya kamata ku yi hankali da alkawuran da kuke dauka,” inji shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel