Wike ga 'yan siyasa: Talakawa sun gaji, ku daina yi musu alkawuran karya

Wike ga 'yan siyasa: Talakawa sun gaji, ku daina yi musu alkawuran karya

- Gwamnan jihar Ribas ya gargaadi 'yan siyasar Najeriya da su daina daukar alkawuran karya

- Ya kuma zargi gwamnatin tarayya mai ci da yaudarar 'yan Najeriya da alkawuran da ba za a iya cikawa ba

- Hakazalika ya yabawa jam'iyyar adawa ta PDP kan samar da kayan more rayuwa ga al'ummar jihar Ribas

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya gargadi ‘yan siyasa a kasar nan kan yin alkawuran karya ga talakawan Najeriya yayin neman zabe a ofisoshin gwamnati, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Ya yi wannan gargadin ne a ranar Asabar a Bori, hedikwatar karamar hukumar Khana ta jihar Ribas.

“Lokaci ya yi; lokacin da idan kuka yi wa mutane alkawari, dole ne ku cika alkawarin. Don haka, ya kamata ku yi hankali da alkawuran da kuke dauka,” inji shi.

A cewar gwamnan, tuni ‘yan Najeriya suka gaji da alkawuran banza da 'yan siyasa ke yi kafin lokacin zabe.

KU KARANTA: Rahoto: Biliyoyin kudin da Najeriya ke tafka asara duk shekara a gyaran bututun mai

Wike ga 'yan siyasa: Talakawa sun gaji, ku daina yi musu alkawuran karya
Wike ga 'yan siyasa: Talakawa sun gaji, ku daina yi musu alkawuran karya Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya yi fatan cewa a shekarar 2023, babu wani dan siyasa da zai iya babakeren sakamakon zabe a kowane yanki na kasar.

Gwamna Wike ya kara da cewa yin magudi ba zai ma yiwu ba ta hanyar amfani da jami'an tsaro, saboda masu zabe sun kara wayewa don bijirewa magudin zabe.

Ya zargi jam'iyya mai ci ta APC karkashin jagorancin Gwamnatin Tarayya da rikita yanayin mutanen kasar.

Gwamnan ya yi zargin cewa gwamnatin ta gaza cika dukkan alkawuran da ta daukar wa mutane tun lokacin yakin neman zabe na shekarar 2015.

Ya kuma yaba wa jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Ribas kan samar da kayayyakin more rayuwa a sassan jihar.

“Lokaci ya yi da ba za mu iya sake sauraran alkawuran karya na 'yan siyasa ba, kamar abin da jam’iyya mai mulki ke yi a yau.

“Lokacin da suka zo a 2015, sun gaya mana cewa naira da dala za su daidaita kuma a yau, menene kwatankwacinsu?

"Sun ce za su samar da ayyukan yi, amma Najeriya ce ke kan gaba wajen yawan marasa aikin yi a Afrika - 33% cikin 100%; me yasa ba za a samu tashin hankali ba? " gwamnan ya tambaya.

Gwamna Wike yayi magana ne yayin taron yakin neman zaben PDP na zaben kananan hukumomin da aka shirya gudanarwa a ranar 17 ga Afrilu.

A wurin taron, gwamnan tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar sun karbi wasu sabbin mambobi daga jam'iyyar APC, karkashin jagorancin tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Ribas, Befil Nwile.

KU KARANTA: Magance tsaro: An kammala horar da 'yan sandan jiha 704 na jihar Kano

A wani labarin, Dattijo dan kasa Alhaji Tanko Yakasai, ya ce zaben Manjo Janar Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasar shi ne babban kuskure da ‘yan Najeriya suka tafka a 'yan shekarun nan.

Yakasai, wanda ya yi magana ta musamman ga Sunday Tribune, ya ce ya san cewa Buhari ba shi da iko da kuma iyawar isar da magance matsalolin kasar.

“Ban taba goyon baya kuma ba zan goyi bayan Buhari ba. Na san Buhari ba shi da kwarewar da zai iya mulkin kasar nan. Ban taba canza ra'ayina game da rashin cancantarsa ta shugabancin kasar nan ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.