Zulum da Sanatocin Borno sun ziyarci CDS da COAS kan batun Boko Haram

Zulum da Sanatocin Borno sun ziyarci CDS da COAS kan batun Boko Haram

- Gwamnan jihar Borno ya ziyarci shigaban hafsun sojojin a babban birnin tarayya Abuja

- Gwamnan ya kai ziyar ne ga shugaban a wata tawaga da ya hada ciki har da sanataoncin jihar

- Ya kuma ziyarci shugaban sojin kasa na Najeriya kan batun hare-haren Boko Haram a Borno

Gwamnan jihar Borno, Zulum, a ranar Litinin, ya jagoranci sanatocin da ke wakiltar jihar a majalisar dokoki ta kasa, suka ziyarci babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor, da kuma shugaban hafsoshin sojan kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru a Abuja.

Zulum, sanata Kashim Shettima (Borno ta Tsakiya), Mohammed Ali Ndume (Borno ta Kudu) da Abubakar Kyari (Borno ta Arewa), tare da shugaban rikon Borno na APC, Ali Dalori, sun gana da shugabannin ne kan hare-haren da kungiyar Boko Haram ta kai a wasu yankuna na jihar.

Dukkan ziyaran an yi su ne daban-daban kuma a cikin kowanne, an gudanar da tattaunawar ta sirri, Vanguard News ta ruwaito.

Dukkan ziyaran an yi su ne daban-daban kuma a cikin kowanne, an gudanar da tattaunawar ta sirri.

KU KARANTA: Mutanen gari sun kona wasu 'yan bindiga kurmus da ransu a jihar Katsina

Zulum da Sanatocin Borno sun ziyarci CDS da COAS kan batun Boko Haram
Zulum da Sanatocin Borno sun ziyarci CDS da COAS kan batun Boko Haram Hoto: independent.ng
Asali: UGC

Kafin daya daga ciki, Zulum ya kai ziyarar gaisuwa a ofishin shugaban sojojin, yana mai godewa sojoji bisa kishin kasa, sadaukarwa da jajircewa a kokarin hada hannu don dawo da zaman lafiya a Borno.

Gwamnan duk da haka ya yi kira ga sojojin Najeriya da su ci gaba da inganta yarda tsakanin jama'a, gwamnati da sojoji.

“Dole ne muyi duk mai yuwuwa don inganta yarda tsakanin mutane, gwamnati, da sojoji.

"Ya kamata mu hada kai, abu daya da ya kamata mu yi shi ne tabbatar da ayyukan da ake gudanarwa ya dore kuma manoma na iya komawa yankunansu na gona don mu rage dogaro da taimakon abinci wanda ba mai dorewa ba ne.

"Za mu bai wa sojoji dukkan goyon bayan da suke bukata, kuma za mu ci gaba da tattaunawa da ku, da fatan za a shawo kan wannan matsalar cikin kankanin lokaci ” in ji Zulum.

Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ya yabawa gwamna Zulum bisa gagarumar goyon bayan da yake baiwa sojoji tare da bayyana ziyarar a zaman da ya dace. Ya lura cewa irin wannan ziyarar tana ba da kofa don musayar ra'ayi mai amfani.

KU KARANTA: Dr. Isa Ali Pantami ya yi martani kan rubutun da aka yi akansa na hannu a Boko Haram

A wani labarin daban, Kimanin mutane 704 daga kananan hukumomi 34 na jihar Kano da aka zaba domin yin aiki karkashin shirin dan sandan jiha, an kammala horar dasu, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa rukunin, wanda aka horar a Kwalejin ’Yan sanda da ke Kaduna, ya kunshi mutane 15 daga kowace daga cikin kananan hukumomin 44 na jihar.

A ranar Lahadin da ta gabata ne Gwamna Abdullahi Ganduje ya kaddamar da ma'aikatan a Kano kuma ya taya su murnar kammala wannan horon.

Asali: Legit.ng

Online view pixel