Mutanen gari sun kona wasu 'yan bindiga kurmus da ransu a jihar Katsina
- Rahotanni sun bayyana yadda wasu fusatattun mazauna suka kashe 'yan bindiga suka kuma konesu
- 'Yan bindigan sun kai hari ne wani yankin jihar Katsina, inda suka hadu da gamon ajalinsu
- A wani rahoton kuwa, 'yan bindigan sun hallaka mutane 3 a wani harin ranar Asabar da ta gabata
Wasu rahotanni sun ce wasu gungun mutane sun kashe tare da kone wasu mutane uku da ake zargin ‘yan bindiga ne a garin Magamar Jibia da ke karamar hukumar Jibia a Katsina.
Lamarin ya faru ne lokacin da wasu ‘yan bindiga suka mamaye garin da misalin karfe 11:25 na daren ranar Lahadi.
Wani mazaunin garin ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa ’yan bindigan sun kutsa kai cikin gidan wani mutum da ba a bayyana sunansa ba, wanda ya yi kukan kura mazauna garin kuma suka tattara suka yi wa 'yan bindigan kawanya.
Wani shugaban al’umma a Jibia wanda ya bayyana cewa sun samu rahoton cewa ’yan bindigan suna shirin kai hari, wanda hakan ya sa suka sanar da dukkan al’umman da ke kusa da su kasance cikin shirin ko ta kwana.
KU KARANTA: Dr. Isa Ali Pantami ya yi martani kan rubutun da aka yi akansa na hannu a Boko Haram
"Na ga gawarwakin mutane biyu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kone ta yadda ba za a iya gane su ba kuma aka jefar da su a mahadar Magama, amma mutum na uku, wanda aka ce yana sanye da kayan sojoji, an ce 'yan sanda sun tafi da shi," in ji shi.
A wani labarin makamancin wannan, wasu ‘yan bindiga sun kashe wasu mutane hudu a daren Asabar a kauyen 'Yar Marafa, yankin 'Yar Malami da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.
A cewar wani mazaunin garin, wadanda lamarin ya rutsa dasu sun hada da Lawal Damfuge, Samaila Namoali, Musdafa Senior da Ado Lafate.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigan sun afka wa kauyen ne a daren Asabar inda suka fara harbe-harbe.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na Katsina, SP Gambo Isah, har yanzu bai tabbatar da faruwar lamarin ba.
KU KARANTA: Wike ga 'yan siyasa: Talakawa sun gaji, ku daina yi musu alkawuran karya
A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta ceto mutane 15 da aka sace tare da kwato shanu 32, The Nation ta ruwaito.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Mohammed Jalige, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi a Kaduna.
Jalige ya ce a ranar 9 ga Afrilu da misalin karfe 3:25 na yamma, wasu ‘yan bindiga sun tare hanyar Buruku Birnin Gwari da ke kusa da dajin Unguwan Yako a kokarinsu na yin garkuwa da mutanen da ke cikin a motoci guda biyu kirar Volkswagen.
Asali: Legit.ng