'Yan bindiga sun halaka mutane, sun ƙona gidaje da motocci a Kaduna

'Yan bindiga sun halaka mutane, sun ƙona gidaje da motocci a Kaduna

- Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun halaka mutum biyu a karamar hukumar Zangon Kataf a Kaduna

- Maharan sun kuma kona gidaje guda bakwai, sannan sun kona mota daya da babur guda daya

- Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Mista Samuel Aruwan ne ya tabbatar da harin

'Yan bindiga, a ranar Litinin sun kashe mutane biyu a karamar hukumar Zangon Kataf da ke jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Mr Samuel Aruwan ya tabbatar da kisar cikin wata sanarwa da ya fitar a Kaduna.

DUBA WANNAN: Hotunan gidajen da 'yan bindiga suka kona a Ondo saboda 'yan garin sun bawa jami'an tsaro bayannan sirri

'Yan bindiga sun halaka mutane, sun kona gidaje da motocci a Kaduna
'Yan bindiga sun halaka mutane, sun kona gidaje da motocci a Kaduna. Hoto: @TheNationNews
Asali: Facebook

"Hukumomin tsaro sun ruwaito cewa yan bindiga sun kai hari kauyen Wawan Rafi II a karamar hukumar Zangon Kataf a safiyar yau.

"A cewar rahoton, mutane biyu sun riga mu gidan gaskiya, wani mutum da dansa mai shekaru bakwai.

"Kazalika, an kona gidaje bakwai da mota daya kuma babur a yayin harin," in ji Aruwan.

KU KARANTA: El-Rufai ya bayyana dalilansa na rage ma'aikata a Kaduna

Ya kara da cewa an tura jami'an tsaro zuwa garin domin su tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Aruwan ya ce jami'an tsaro sun gano gidan harsashi 7.62mm a wurin da aka kai harin.

"Kawo yanzu, an gano gawarwaki biyu. Za a cigaba da yi wa mutane bayani nan gaba," in ji shi.

A bangare guda kun ji cewa shahararren Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, ya yi ikirarin cewar wadansu daga cikin masu fada-a-ji wanda ya hada da 'yan siyasa da Malaman addini, su ne asalin ma su daukar nauyin rashin tsaro a wasu sassa na kasar nan .

Ya yi wannan bayani ne a Abuja a yayin kaddamar da wata littafi da aka wallafa kamar yadda Vangaurd ta ruwaito.

Khalid ya yi ikirarin cewar 'yan ta'adda wanda da yawansu matasa ne su na aikata ta'addanci ga al'umma sakamakon mu'amalarsu da sanannu malamai da 'yan siyasa wadanda su ke son kasar ta kone kurmus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel