2023: Ka hakura kawai, ka ba yankin kudu dama - Kungiyar APC ta fadawa Yahaya Bello
- Da wuya Gwamna Yahaya Bello ya cimma kudirinsa na son zama Shugaban kasa a 2023
- Gwamna Bello ya kasance daya daga cikin manyan yan Najeriya da ke hararar kujerar Shugaban kasa Muhammadu Buhari
- Kungiyar APC ta arewa maso tsakiya, ta fadawa Bello da ya bari yankin kudancin kasar ta samar da magajin Buhari a 2023 saboda adalci
An shawarci gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi da ya hakura da kudirinsa na son zama magajin Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa wata kungiya a cikin jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) a ranar Alhamis, 8 ga Afrilu, ta roki gwamna Bello da ya goyi bayan kiraye-kirayen da ake yi na mika shugabancin jam’iyyar na kasa ga yankin arewa ta tsakiya.
KU KARANTA KUMA: Kiristoci sun fi Musulmi tausayi - In ji tsohuwar jarumar Kannywood, Ummi Zeezee
Legit.ng ta tattaro cewa yayin da yake magana a sakatariyar jam'iyyar na kasa a Abuja, kungiyar APC ta arewa ta tsakiya karkashin jagorancin shugabanta, Kassim Muhammad ya yabawa kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar wanda gwamna Mai Mala Buni ke jagoranta.
Ya ce a lokacin da kwamitin ya kammala wa’adin mulkinsa, APC za ta bukaci jajirtacce, mai kuzari kuma gogaggen dan jam’iyya don gudanar da harkokin ta.
Muhammed ya kara da cewa kungiyar ta Arewa ta Tsakiya ta roki Gwamna Bello da ya sake tunani game da kudirinsa na son zama shugaban kasa a 2023, ya kara da cewa zai fi zama daidai a bari yankin kudancin kasar ya samar da shugaban kasa na gaba a 2023.
Jigon na APC ya ce:
“Mun yi imanin cewa amincewa da mika tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyarmu zuwa yankin kudancin kasar zai bunkasa daidaito da adalci na siyasa. Mun yi imanin cewa gwamnan jihar Kogi dan dimokiradiyya ne na gaskiya wanda ya yi imani da Najeriya daya."
Ta kuma yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da dukkan gwamnonin APC da sauran manyan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da su ci gaba da marawa Gwamna Buni baya domin samun nasarar aikinsa na saita jam'iyyar don zabukan da ke tafe.
KU KARANTA KUMA: Buhari bai halarci taron kaddamar da littafin uwar gidansa Aisha ba
A wani labarin, tsohon Ministan Labarai, Farfesa Jerry Gana da magoya bayansa a jiya Laraba, 7 ga watan Afrilu, sun koma Jam’iyyar PDP.
Da yake jawabi ga mambobin jam’iyyar a liyafar bikin dawowarsa PDP a hukumance a garin Bida da ke jihar Neja, Gana ya ce kasar nan ta tabarbare kuma tana bukatar ceto cikin gaggawa.
Gana, wanda mamba ne na kwamitin amintattu (BoT) na PDP a watan Maris, 2018, ya sauya sheka daga PDP ya kuma hade da jam’iyyar Social Democratic Party (SDP).
Asali: Legit.ng