Kiristoci sun fi Musulmi tausayi - In ji tsohuwar jarumar Kannywood, Ummi Zeezee

Kiristoci sun fi Musulmi tausayi - In ji tsohuwar jarumar Kannywood, Ummi Zeezee

- Tsohuwar jarumar nan ta Kannywood, Ummi Zeezee ta ce Kiristocin Najeriya sun fi Musulmi tausayi

- A cewar Ummi ta gane hakan ne bayan ibtila'in da ya fada mata da damfarar da wani Inyamuri yayi mata na kudi har miliyan 450

- Ta ce a lokacin da labari ya bazu kan haka, yan uwanta Musulmi na ta zaginta yayinda Kiristoci suka nuna mata tausayi da jin kai

Fitacciyar tsohuwar jarumar nan ta Kannywood, Ummi Ibrahim wacce aka fi sani da Zee-zee ta bayyana cewa ‘yan Najeriya waɗanda ba Musulmi ba sun fi Musulmi jin ƙai.

Zee-zee ta bayyana cewa ta gane haka ne daga abin da ya faru a gare ta a lokacin da ta yi barazanar kashe kanta saboda damfarar da aka yi mata na kuɗi masu yawa har naira miliyan 450.

Ta ce a lokacin da abin ya faru, yawancin Hausawa ko ‘yan Arewa Musulmi sun ƙaryata sannan wasu sun zagin ta, amma su kuwa ‘yan Kudu waɗanda ba Musulmi ba sune suka tausaya mata da jajanta mata.

Kiristoci sun fi Musulmi tausayi - In ji tsohuwar jarumar Kannywood, Ummi Zeezee
Kiristoci sun fi Musulmi tausayi - In ji tsohuwar jarumar Kannywood, Ummi Zeezee Hoto: ummizeezee
Source: Instagram

Har ila yau tsohuwar jarumar ta yi Allah wadai da waɗanda su ka zage ta ko su ka ƙaryata ta a kan wannan lamari.

KU KARANTA KUMA: PDP tayi babban kamu yayinda Farfesa Jerry Gana da magoya bayansa suka sauya sheka zuwa jam’iyyar

A makon da ya gabata ne dai tsohuwar jarumar ta bayyana cewa wani Inyamiri ya zambace ta zunzurutun kuɗi har naira miliyan 450, kuma faruwar hakan ya sanya ta yanke hukuncin gara ma ta kashe kan ta ta huta.

A wani wallafa da tayi a shafinta na Instagram ta ce:

“Salam ‘to Nigerians’, ina son ku ban dama in gode muku a bisa jaje da ku ka min ta hanyar kira na a waya da aiko min da ‘text’ dangane da damfara na da aka yi na kuɗi masu yawa naira ‘million’ ɗari huɗu da hamsin a kan wani ‘business’ da za mu yi na saye da sayarwa na ƊANYEN MAI da wani Inyamuri da ke Lagos.

“Ya damfare ni a kan ‘business’ da za mu yi da shi, amma maƙiya na saboda jahilci da hassada sai su ke cewa ba wani damfara na da aka yi, ƙarya ne. To Aljanna za a sa ni a ciki ko ko zunubai na za a yafe min da zan yi ƙarya in ce an damfare ni bayan kuma ba a damfare ni ba?

“To ya kamata mu Hausawa mu koyi son junan mu domin duk Musulmi ɗan’uwan Musulmi ne.

“Da aka damfare ni, akwai wani ‘page’ mai suna @instablog9ja, su ma sun yi ‘posting’ damfara na da aka yi, amma wallahi da na shiga ‘page’ ɗin ban ga ana zagi na ba, sai addu’a kawai da ake min da kuma ban haƙuri a kan damfara na da aka yi. Wasu ma ‘direct’ su ka dinga kira na su na jajanta min.

“Kuma fa shi mai ‘page’ ɗin instablog9ja ɗin wallahi da shi da ‘followers’ ɗin nasa duk yawanci arna ne ‘yan Kudu ammah anan arewa kuma duk wani pages da akayi posting damfarana da akayi to zagina kawai akeyi.

"Abun ya ban haushi ba zagina da akayi bane ya ban haushi ba abunda ya ban haushi shine ace ina musulma kaddara ya sameni ammah sai arna ne Wanda addinin mu ba daya ba sune zasu nuna alhinin su akan damfarana da akayi?

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban karamar hukuma a Ribas

"Sai yanzu na fahimci arnan nigeria wallahi sunfi musulman nigeria tausayi dan haka Allah wadaran musulmai masu irin wannan mummunar zuciyar."

A baya mun ji cewa Ummi Zeezee, ta ce ta shiga kangin rayuwa, inda har ta kan ji kamar ta kashe kanta.

A ranar Asabar, 3 ga watan Afrilu ne jarumar ta fadi hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram.

Sai dai jarumar wacce ta yi fitattun fina-finai irinsu ”Jinsi,” “Gambiza” da "Tutar So" ta ce kada kowa ya tambaye ta dalilin da ya sa take so ta aikata wannan danyen aiki.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel