Buhari bai halarci taron kaddamar da littafin uwar gidansa Aisha ba

Buhari bai halarci taron kaddamar da littafin uwar gidansa Aisha ba

- Ko sama ko kasa ba a ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a wajen taron kaddamar da littafin Uwar gidansa Aisha ba

- Buhari wanda a yanzu haka yake birnin Landan don ganin likitansa ya samu wakilcin Farfesa Ibrahim Gambari, Shugaban Ma’aikatansa

- Daga cikin manyan mutanen da suka hallara harda mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da matarsa, Dapo

Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya cikin manyan mutanen da suka hallara a dakin taro na gidan gwamnati, Abuja, wurin taron kaddamar da littafin Aisha, matar sa.

Littafin, “Aisha Buhari, Being Different”, babbar mataimakiya ta musamman ga shugaban kasa kan harkokin mulki da mata, Dokta Hajo Sani, ce ta wallafa shi.

KU KARANTA KUMA: 2023: Daga karshe Arewa ta bayyana matsayinta akan zaben shugaban kasa, tayi watsi da tasirin addini

Babbar magana: Buhari bai halarci taron kaddamar da littafin uwar gidansa Aisha ba
Babbar magana: Buhari bai halarci taron kaddamar da littafin uwar gidansa Aisha ba Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Buhari, wanda a yanzu haka yake Landan domin duba lafiyarsa, ya samu wakilcin Farfesa Ibrahim Gambari, Shugaban Ma’aikatansa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo da matar sa, Dolapo, na daga cikin manyan bakin da suka halarci taron.

Asiwaju Bola Tinubu, shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, shine shugaban taron yayin da biloniya 'yar kasuwa, Folorunsho Alakija, ita ce babbar bakuwa ta musamman.

KU KARANTA KUMA: Fitattun 'yan siyasa 10 a Najeriya masu sarautar gargajiya

A baya mun ji cewa, babban mai kudin Afrika, Aliko Dangote, zai jagoranci fitattun ‘yan siyasa da manyan Najeriya zuwa wajen bikin kaddamar da littafin Aisha Buhari.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa za a kaddamar da wani littafin da aka rubuta a game da uwargidar shugaban kasa, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari.

A lokacin da Mai dakin shugaban kasar ta dawo Najeriya daga kasar tarayyar Larabawa, UAE, ana shirin kammala shirye-shiryen kaddamar da wannan littafi.

A wani labarin, a ranar Laraba mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana dalilin da ya sanya Buhari ya nada Usman Alkali a matsayin sabon sifeta janar na 'yan sanda.

A cewar Osinbajo, Alkali yafi kowannensu matsayi, hakan ne ya bayar da damar da ya sanya aka nada shi a matsayin sabon IGP din.

Mataimakin shugaban kasa ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja yayin da yake nada Alkali a sabuwar kujerar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel