Abin da ‘Yan Najeriya su ke fada game da littafin Aisha Buhari da aka kaddamar a Aso Villa

Abin da ‘Yan Najeriya su ke fada game da littafin Aisha Buhari da aka kaddamar a Aso Villa

- A yau aka kaddamar da littafin tarihin Uwargidar Najeriya, Aisha Buhari

- An yi bikin fito da littafin ne a lokacin da shugaban kasa ya ke kasar Ingila

- Jama’a sun tofa albarkacin bakinsu game da wannan sabon littafi a Twitter

‘Yan Najeriya da-dama da ke amfani da kafafen yada labarai da sada zumunta sun yi magana game da littafin Aisha Buhari da aka kaddamar.

A yau ne Hajo Sani ta kaddamar da littafin da ta rubutu a kan rayuwar uwar gidanta, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, inda aka yi biki a Aso Villa.

Dinbin ‘yan siyasa da attajirai da manyan kasa sun samu halartar bikin kaddamar da wannan littafi mai suna “Aisha Buhari, ta fita dabam” dazu.

KU KARANTA: Rikici ya kunno kai a PDP tsakanin Kwankwaso da wani Gwamna

Daily Trust ta tattaro wasu daga cikin martanin da mutane su ke yi game da wannan sabon littafi da aka fitar a lokacinn da shugaban kasa ba ya nan:

FS Yusuf ya ce: “Akalla Patience Jonathan ta yi zamanta, ta na buga jagwalgwalon turancinta a kan kashe-kashen da aka yi a kasar nan. Aisha Buhari kuwa ta yi zamanta ne a Dubai na wata da watanni yayin da ake hallaka mata da yara, ta na dawo wa, ta dauko batun kaddamar wa ‘Yan Najeriya littafi su karanta.”

Jamie Fash cewa ya yi: “Uwargidar shugaban Najeriya ta na neman samun kudin ta ne kurum. An dade ana yi babu ita, shiyasa ta kinkimo maganar kaddamar da littafi domin ta cika aljihunta.”

Okey D General ya ce: "Aisha Buhari ta na kaddamar da littafinta yau, mai gidanta, Buhari ya na Landan ya na huta wa. Ta ina gidan da ba daidai yake ba, zai iya dinke Najeriya?

KU KARANTA: Ina 'dan sarara wa ne a Ingila - Inji Buhari

Abin da ‘Yan Najeriya su ke fada game da littafin Aisha Buhari da aka kaddamar a Aso Villa
Bikin kaddamar da littafin Aisha Buhari Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Shi kuwa wani Bawan Allah mamaki yake yi da aka ce Aisha Buhari ta na cikin wadanda su ka karfafa wa shugaba Buhari shiga cikin harkar siyasa.

Dazu kun ji jagoran jam'iyyar APC a Kudu maso yammacin Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu, ya yabi Hajiya Aisha Buhari wajen kaddamar da littafin na ta.

Bola Tinubu ya bayyana cewa uwargidan shugaban ƙasar ba ta da tamka, ya ce irin ayyukan da ta ke yi a matsayinta sun nuna ba za a sake yin irinta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel