2023: Daga karshe Arewa ta bayyana matsayinta akan zaben shugaban kasa, tayi watsi da tasirin addini
- Kungiyar dattawan Arewa sun ce ba za su yi amfani da ra’ayin addini wajen goyon bayan dan takarar shugaban kasa a 2023 ba
- Shugaban NEF, Ango Abdullahi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, 7 ga watan Afrilu
- Abdullahi ya bayyana cewa sun koyi babban darasi a zabin da suka yi na dan takarar shugaban kasa a baya
Farfesa Ango Abdullahi, shugaban kungiyar dattawan Arewa (NEF), ya bayyana cewa arewa ba za ta yi amfani da kabila da addini ba wajen zaben shugabanni a 2023.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa yace ‘yan arewa sun koyi darasi mai tsadar gaske.
Legit.ng ta tattaro cewa Abdullahi ya bayyana cewa babu wani dan arewa da za a ba tabbacin samun goyon bayan yan arewa don kawai ya kasance dan yankinsu.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Mohammed Adamu ya sauka a hukumance, ya mika mulki ga sabon IGP Usman Baba
Shugaban na arewa ya ce yanayin abubuwa sun koya wa yankin dabi'un bin diddigin bayanai, halaye da jin kai.
Ya yi magana a Kaduna a ranar Laraba, 7 ga Afrilu, a matsayin jagoran taron jama'ar Arewa kan shinge tsakanin mutane da shugabanninsu.
Abdullahi ya ce:
“Masu jefa kuri’ar Arewa sun goyi bayan‘ yan kudu uku, Abiola, Obasanjo da Jonathan don cin nasara a baya, biyu daga cikinsu kan ‘yan arewa.
“Masu jefa kuri’ar Arewa suna da wayewa da kuma sani.
“Masu jefa kuri’ar Arewa suna da wayewa da sanin nauyin da ke kansu. Sun koya, wataƙila fiye da yawancin 'yan Najeriya, cewa kabilanci da addini kawai basa sa shugabanni su zama na kwarai. Ba za su yarda a kara raunana su ba saboda haka sun yi watsi da hakkoki iri daya da duk 'yan Najeriya ke da shi."
Ya kara da cewa ‘yan siyasar da ke son‘ yan arewa su zabi wani toh su kara kaimi sannan su gamsar da ‘yan arewa yadda‘ yan takarar su za su inganta tsaro, tattalin arziki da zamantakewar arewa da kasar.
Abdullahi ya ci gaba da cewa yin amfani da sake fasalin kasa a matsayin wata barazana ko kuma wata yarjejeniya ta mulkin karba-karba zai ruguza ayyukan sake fasalin kasar da kuma jefa kasar nan cikin matsala.
KU KARANTA KUMA: Mallam dogo: Baiwar tsayi da Allah yayi wa wani saurayi ya haifar da cece-kuce a soshiyal midiya
Amma, ya shawarci dukkan 'yan siyasar Najeriya da su duba su ga yadda kasa ta sauya daga karkashin kafafunsu.
A wani labarin, wani kudiri da ke gaban majalisar wakilan tarayya ya na neman halattawa mata amfani da hijabi a wajen aikin gidan soja da sauran aikin khaki.
Jaridar Punch ta bayyana cewa Honarabul Saidu Abdullahi mai wakiltar Bida/Gbako/Katcha a majalisar wakilan tarayya ne ya gabatar da kudirin.
Wannan kudiri ya samu karbuwa, har ya kai mataki na biyu a zauren majalisar wakilan kasar.
Asali: Legit.ng