Dangote, Tinubu da sauran manyan kasa za su taru a Aso Villa wajen bikin littafin Aisha Buhari

Dangote, Tinubu da sauran manyan kasa za su taru a Aso Villa wajen bikin littafin Aisha Buhari

- Dr. Hajo Sani ta rubuta wani littafi game da rayuwar Aisha Buhari

- Za ayi bikin kaddamar da wannan littafi ne a fadar Shugaban kasa

- Bola Tinubu, Aliko Dangote, da Ministoci za su halarci wannan taro

Babban mai kudin Afrika, Aliko Dangote, zai jagoranci fitattun ‘yan siyasa da manyan Najeriya zuwa wajen bikin kaddamar da littafin Aisha Buhari.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa za a kaddamar da wani littafin da aka rubuta a game da uwargidar shugaban kasa, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari.

A lokacin da Mai dakin shugaban kasar ta dawo Najeriya daga kasar tarayyar Larabawa, UAE, ana shirin kammala shirye-shiryen kaddamar da wannan littafi.

KU KARANTA: Obasanjo ya caba ado kamar wani 'Dan saurayi

Rahotanni sun tabbatar da cewa abin da ya rage shi ne ayi bikin kaddamar da littafin a fadar shugaban kasa na Aso Villa ranar Juma’a da karfe 9:00 na safe.

Jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, shi ne zai shugabanci wannan taro da za ayi. Attajirar nan, Folorunsho Alakija, ita ce babbar bakuwar ranar.

Aliko Dangote, Abdusamad Rabiu, Prince Authur Eze, Hajiya Bola Shagaya, Femi Otedola, Tony Elumelu, su na cikin manyan attajiran da za su halarci taron.

Manyan kasa da aka gayyata wajen bikin su hada da; Sarkin Ife, Adeyẹ́yẹ̀ Ẹnitan Ògúnwusi; Sultan Muhammadu Sa’ad Abubakar III da Mai martaba Appolus Chu.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta bukaci a yi wa Najeriya addu'a

Dangote, Tinubuu da sauran manyan kasa za su taru a Aso Villa wajen bikin littafin Aisha Buhari
Aisha Muhammadu Buhari Hoto: www.theeagleonline.com

Har ila yau surukin Buhari, Mohammadu Indimi, da Jim Ovia, Kessignton Adebutu, Daisy Danjuma, Idahosa Wells Okunbo duk za su samu halartar bikin.

Ministocin da za su bada masaukin baki su ne Ministan babbar birnin tarayya, Mohammad Bello da takwararsa, Ministar harkokin mata ta kasa, Pauline Tallen.

Dr. Hajo Sani ce ta rubuta wannan littafi da babban malami, Farfesa Fatai Aremu ne ya yi wa ta’aliki.

Ku na sane cewa Uwargidan shugaban kasar ta dawo gida Najeriya ne bayan watanni shida a birnin Dubai, hakan ya sa aka dade ana tambayar ina ta shiga.

Uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta tafi Dubai ne tun bayan auren diyarta, Hanan Buhari, wanda aka yi a Satumban 2021, ba a ganta ba sai kwanaki.

Source: Legit

Online view pixel