Jerin jami'an da suka rike matsayin Sufeta-Janar na 'yan sanda daga 1999 - 2021
Biyo bayan cece-kuce da ya shahara a kafafen sada zumunta kan karin wa'adin tsohon IGP, an sake sabon nadi
- A makon nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da nadin sabon IGP na rikon kwarya
- Rahoton Legit.ng Hausa ya tattaro jerin wadanda suka rike matsayin IGP daga shakarar 1999 zuwa 2021
Legit.ng Hausa ta tattaro rahoto kan jami'an 'yan sandan da suka rike matsayin IGP tun 1999 har zuwa bana; 2021.
1. IGP Musiliu Smith
Mista Musiliu ya zama IGP na 'yan sandan Najeriya a watan Mayun 1999, ya kuma yi ritaya a watan Maris na 2002.
2. IGP Mustapha Balogun
Balogun ya zama IGP a watan Maris na 2002, ya kuma yi ritaya a watan Janairun 2005 sakamakon zargin wata badakala, kamar yadda Wikipedia ta tattaro.
3. IGP Sunday Ehindero
Ehindero ya karbi Balogun a watan Janairun 2005, ya yi ritaya a 2007.
4. IGP Mike Okiro
Okiro ya kasance a IGP na 'yan sandan Najeriya daga 2007 zuwa 2009 in da ya yi ritaya.
KU KARANTA: Tsadar Siminti ta sa wani dan Najeriya gina da robobin ruwa a Kaduna
5. IGP Ogbonna Onovo
Ya karbi matsayin IGP a watan Yulin 2009 ya kuma yi ritaya a watan Satumban ta 2010.
6. IGP Hafiz Ringim
Ringim ya zama IGP na 'yan sanda a 2010, ya mika kuma matsayin na IGP ga Mohammed Dikko a 2012.
7. IGP Mohammed Dikko
Shi kuwa Dikko daga 2012 ya kai har 2014 kafin a karbe shi.
8. IGP Suleiman Abba
Suleiman Abba aka nada bayan Dikko a 2014, ya kuma mika matsayin ga abokin aiki Solomon Arase a 2015.
9. IGP Solomon Arase
Ya karbi matsayin Abba a watan Afrilun 2015, ya yi ritaya a watan Yunin 2016.
10. IGP Ibrahim Idris
Ibrahim Idris ya rike matsayin IGP tun farkon hawan shugaba Buhari mulki a 2015, ya mika matsayin IGP ga Mohammed Adamu a 2019.
11. IGP Mohammed Adamu 2019-2021
Mohammed Adamu da aka sallama a makon nan, ya fara aiki a matsayin IGP tun a watan Janairun 2019, ya mika matsayin ga sabon jini DIG Usman Baba a makon nan; 6 ga watan Afrilun 2021.
12. DIG Usman Baba
DIG Usman Alkali Baba, ya karbi Mohammed Adamu bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya sanar sauya tsohon IGP a rana 6 ga watan Afrilun 2021.
KU KARANTA: Wani kamfanin Amurka ya nemi afuwa kan saka hoton masallaci a rigar mawaki
A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda ta cafke wani mai suna Cletus Nwachukwu Egole wanda aka fi sani da Alewa, wani fasto a cocin Holy Blessed Trinity Sabbath, da ke Orlu, a jihar Imo, dangane da harin da aka kai wa jami’an tsaro a sassan Kudu maso Gabas.
Sama da jami'an tsaro 15 aka harbe har lahira a wasu hare-hare daban-daban a cikin yankin a cikin watan Maris kadai, Daily Trust ta ruwaito.
An kona ofisoshin 'yan sanda da dama a hare-haren yayin da aka kwashe makamansu a matsayin ganima.
Asali: Legit.ng